Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce, makirce-makircen da Jam’iyyar APC mai mulkin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ke yi na ƙwace Jihar Ribas da ƙarfin tsiya ya kai intaha na ƙoƙarin ƙwace jihar da ƙarfin tsiya daga PDP, amma ta ce hakan ba zai cimma nasara ba.
A ranar Laraba ne shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Ribas suka buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci a jihar, bisa zargin cewa jihar na cikin yanayin tashin-tashina.
Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC, Tony Okocha ne ya yi wannan kiran a yayin wani taron manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar.
Ya ce: “Jihar Ribas na fama da yaƙi, kuma an san mutanen da ke da alhakin rikicin da ya yi sanadin asarar rayuka.
“Gwamnan ba shi da wani taimako, ‘yan sanda ba su da komai. Don haka jam’iyyar APC a jihar Ribas na kira da a kafa dokar ta-ɓaci a jihar Ribas a matsayin hanyar da za ta magance tashe-tashen hankula, da kuma tada zaune tsaye a jihar. Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki kan hakan,” in ji Mista Okocha.
Sai dai da take mayar da martani, PDP ta ce a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, cewa furucin Mista Okocha ya fallasa aniyar APC na haddasa rikici a jihar mai arzikin man fetur.
Ya jaddada cewa jihar ta kasance matattarar jam’iyyar PDP kuma duk wani yunƙurin ƙwace mulki da ƙarfi za a yi watsi da shi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Hankalin jam’iyyar PDP ya karkata ga wani taron manema labarai mai cike da ruɗani da shugaban riƙo na jam’iyyar All Progressiɓes Congress na jihar Ribas, Tony Okocha ya yi, inda ya sake tunanin cewa al’ummar Ribas za su so jiha kamar yadda aka bayyana a zaɓen gwamna wanda ya samar da Gwamna Siminalayi Fubara za a iya juyar da tunanin APC.
“Wannan ɓacin rai da Tony Okocha ya yi ya ƙara fallasa mugun makircin da jam’iyyar APC ta yi a jihar Ribas, inda ta nemi hanyoyin tada rikici, da ƙarfin tsiya ta hanyar juyin mulkin dimokuraɗiyya, da kuma kafa tsarin mulkin dimokaraɗiyya a jihar Ribas wanda ya saɓawa sashe na 1 ƙaramin sashe na 2 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya, 1999 (kamar yadda aka gyara).
“Yin amfani da kalmar ‘yaƙi’ da Mista Okocha ya yi a cikin furucinsa na rashin tunani yana nuna a fili wata muguwar manufa wadda suka tsayu akan ta kuma za ta ci gaba da samun turjiya daga mutanen jihar Ribas.
“Ya kamata jam’iyyar APC a jihar Ribas ta lura cewa makircin da take yi na haddasa rikici da kuma ƙwace jihar da ƙarfi ya ci tura. Jihar Ribas babbar madaldalar PDP ce, kuma jama’a na goyon bayan gwamnatin PDP a jihar.
“Jam’iyyar PDP tana kira ga Gwamnatin Tarayya da ma shugabannin Jam’iyyar APC na ƙasa da su gaggauta ɗaukar mataki tare da gargaɗin Mista Tony Okocha da ya daina zama wakilin tashe-tashen hankula da kuma barazana ga dimokuraɗiyya a Nijeriya.
“Jam’iyyarmu ta buƙaci Babban Sufeton ‘yan sandan ƙasar nan da ya gayyato shugaban riƙo na jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, ya kuma ɗora shi a kansa kan furucin da ya yi, wanda hakan ya zama haɗari a fili kuma a halin yanzu ga ɗorewar dimokuraɗiyya a Nijeriya da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Ribas.
“Ya kamata al’ummar Nijeriya su kuma lura da yadda wannan mutumi ya yi katsalandan, wanda ayyukansa da maganganunsa na iya yin illa ga tsaron ƙasar bakiɗaya.
“PDP, a karo na goma sha uku, tana gargaɗin APC da ta rushe tunanin karɓe jihar Ribas da ƙarfi, saboda yunƙurin da take yi na ɓata ra’ayin jama’a zai ci tura.
