Ƙasar Canada, ta sanya sunan rundunar Juyin-juya hali ta Ƙasar Iran IRGC, cikin jerin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, inda ta buƙaci ‘yan ƙasarta da ke Iran ɗin su fice.
Gwamnatin Kanada ta sanar da hakan ne a ranar Laraba, tana mai bayyana matakin a matsayin wani ɓangare na yakin da Ottawa ke yi da ta’addanci.
‘Yan siyasar ƙasar ta Canada sun jima suna fatana ganin an aiwatar da wannan mataki, wanda ke nufin za a hana dubban manyan jami’an rundunar ta IRGC shiga ƙasar.
Shekaru da dama, ‘yan adawa masu ra’ayin mazan jiya a Canada sun buƙaci Firaminista Justin Trudeau, da ya sanya sunan IRGC cikin jerin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a duniya.
Ministan tsaron Canada Dominic LeBlanc, ya ce Tehran, ta jima tana nuna halin ko-in-kula ga ‘yancin ɗan adam amma lokaci ya yi da za a ɗaga mata yatsa.
Tuni dai, Iran ta yi Allah wadai da matakin na Kanada a matsayin rashin wayewa da kuma rashin iya siyasar duniya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanaani ya ce matakin na Kanada ba zai yi wani tasiri ba kan halastaccen ikon dakarun juyin-juya halin Musulunci na Iran.
