Amurka ta ce a fusace ta ke da Chana kan goyon bayan Rasha a yaƙin Ukraine

Spread the love

Amurka ta cacaki Ƙasar Chana da game da zargin bai wa Rasha tallafi da kuma goyon bayanta a yaƙin da ta ke yi da Ukraine.

Da ya ke bayyana takaicinsa game da batun, sakataren harkokin wajen ƙasar Antony Blinken, ya ce lokaci ya yi da ya kamata duniya ta juyawa Chana baya, har sai ta tsame hannunta daga tallafa wa Rahsa a wannan yaƙi.

A mabambantan lokuta dai, Chana ta sha musanta zargin bai wa Rasha tallafi ta kowaccce fuska game da yaƙin, to sai dai Blinken wanda ke magana gaban wani taron manema labarai tsakanin sa da shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO ya ce a bayyane yake ƙarara cewa Rasha tana samun taimakako daga Chana.

Chana dai, ta bayyana kanta a matsayin ƙasar da ke ƙoƙarin kawo daidaito a yaƙin na Ukraine, kuma ta ce ba bu wani taimako da take yi ga kowane ɓangare, sabanin Amurka da sauran ƙasashen yammacin duniya da suke taimaka wa Kyiɓ don yaƙar Moscow.

Shima da yake nasa jawabi, Jen Stoltenberg ya ce lokaci ya yi da ya kamata Chana ta fuskanci fushi da kuma hukunci, matuƙar ta ci gaba da bai wa Rasha tallafi ko kuma ƙulla alaƙa da ita.

Blinken da kuma Stoltenberg, sun kuma yi fargabar cewa akwai wata sabuwar alaƙa da ake zargin tana shirin ƙulluwa tsakanin Rashan da kuma Koriya ta Arewa, wadda ita ma ba zata haifarwa Ukeraine da mai ido ba.

By ukarofi