Ɗan sanda ya harbe alƙali ana tsaka da shari’a a kotu

Spread the love

Wani babban jami’in ‘yan sandan Kenya ya harbi mai jagorantar shari’a a wata kotun majistare da ke Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.

Ɗan sandan mai muƙamin babban Isfekta ya buɗe wa mai shari’a Monica Kiɓuti wuta jim kaɗan bayan ta yanke wa matarsa hukunci kan wani laifi da ake zarginta da aikatawa.

Rahotonni sun ce jami’in ɗan sandan ya fusata ne bayan da kotun ta ƙi amincewa da buƙatar belin matar tasa.

Daga nan ne, Sufeto Samson Kipchirchir Kipruto, wanda ke jagorantar ofishin ‘yan sanda na Londiani da ke yammacin ƙasar, ya zaro bindigarsa tare da harbe alƙalin inda ya ji mata rauni.

Nan take kuma jami’an ‘yan sanda da ke kotun suka mayar da martani, inda ɗaya daga cikinsu ya harbe tare da kashe mista Kipruto.

Rahoton ‘yan sanda ya nuna cewa uku daga cikin jami’an tsaron da suka mayar da martanin sun samu raunuka a musayar wutar da suka yi da mista Kipruto.

Tuni dai aka garzaya da alƙalin da sauran jami’an ‘yan sandan uku zuwa asibiti domin yi musu magani.

Amma daga baya, Alƙalin Alƙalan Kenya ya ce alƙalin da ɗan sanda ya harba a lokacin da take tsaka da jagorantar shari’a a mutu a asibiti.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Ɗ, Justice Martha K Koome ya ce alƙalin kotun Makadara, Mai shiari’a Monica Kiɓuti ta “rasu sakamakon munanan raunukan da ta samu”.

A ranar Alhamis ne wani babban jami’in ɗan sanda ya harbi Ms Kiɓuti a tsakiyar kotun, lokacin da ta ƙi amincewa da buƙatar bayar da belin matarsa.

Bayan buɗe wa alƙalin wuta ne, ‘yan sandan ta ke ganin kotun suka mayar wa jami’in ɗan sandan mai suna Samson Kipchirchir Kipruto martani, inda suka kashe shi bayan harbin da suka yi masa.

Musayar wutar da ‘yan sandan suka yi da shi ta sa uku daga ciki sun samu raunuka, inda suka karɓar magani a asibiti.

By ukarofi