Kotu ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 30 ga wasu mutane biyu da aka kama suna yin sojan gona a matsayin jami’an hukumar (EFCC.
Dubun jami’an EFCC na bogi, Ugwu Chijioke da Ibrahim Adekunle, ta cika ne a lokacin da suka je domin zartar da wani jabun umarnin kotu a unguwar Lekki da ke Legas a watan Mayun 2021.
Abubuwan da aka kama a hnnun waɗannan jami’an EFCC na bogi sun hada da jabun katin shaidar aiki da rigunan hukumar da kuma takardar umarnin gobi daga Kotun Majistare da ke zamanta a Mushin.
Hukumar ta gurfanar da su a gaban Kotun Laifuka na Musamman da ke Ikeja, kan laifuka biyar na yin damfara, sojan gona, mallakar takardun bogi amfani da kayan EFCC ba bisa ƙa’ida ba.
Bayan sun amsa duk laifukan, Mai Shari’a O.O. Abike-Fadipe ya yanke musu hukundin ɗaurin jimillar shekaru 46 kowannensu.
Alƙalin ya yanke musu hukucin ɗaurin shekara takwas kan laifi na biyar, shekaru bakwai-bakwai a kan laifuka na 1 zuwa na 3, da kuma shekara guda kan laifi na huɗu.
Sai dai alƙalin ya bayyana cewa kirgen shekarun zaman gidan yarin da za su yi zai gudana ne a tare lokaci guda, ba a jere ba.
