Wata mata ‘yar shekara 45 mai suna Abiodun ta banka wa mahaifiyarta ’yar shekara 86 wuta a garin Ondo da ke Ƙaramar Hukumar Ondo ta Yamma a Jihar Ondo.
Abiodun, wadda aka fi sani da ‘Iya Sunday’ ta ce ta ƙona mahaifiyarta ne saboda zargin ta da zamowa silar wahalhalunta a rayuwa.
Wani ganau mai suna Sola Oladele ya bayyana cewa wadda ake zargin ta zo gidan mahaifiyarta ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 5 na safe ta kira ta kafin ta zuba mata man fetur sannan ya banka mata wuta.
Ganau ɗin ya ce, matar da faɗa masa cewa, “Na je gidan mahaifiyata da misalin ƙarfe 4 na safe inda na zauna a waje. Da ƙarfe biyar na safe, na kwaɗa mata kira ta fito. Nan da nan ban tsaya wata-wata ba na zuba mata man fetur a jikinta na banka mata wuta.
“Abin ya fara ne a lokacin da na je wurin wani fasto don ya yi min addu’a, kuma ya gaya min cewa mahaifiyata ce ke bayan abin da ke faruwa da ni a rayuwa. Ban yarda ba da farko. Mahaifiyata ta sake kai ni wurin wata mata don ta bincika min me ke faruwa da ni a rayuwa. Bayan mahaifitar ta tafi, itama matar ta sake faɗa min abin da faston ya faɗi.
“Na ƙona mahaifiyata ne saboda abin da na ji daga wurin Fasto da kuma matar, cewa zan iya tsira daga ƙangin talauci ne kawai idan mahaifiyata ta mutu,” inji ganau.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta sanar da cewa mamaciyar ta rasu ne a ranar Asabar.
Ta bayyana cewa tun da matar ta rasu ne a lokacin da take jinya a asibiti, za a tuhumi wadda ake zargin da laifin kisan kai.
