Rundunar Soji ta hallaka ƙasurgumin ɗan ta’adda a Kaduna

Spread the love

Daga Bala Muhammad

Rundunar Sojin Najeriya, ta ce ta kashe wani sanannen ɗan ta’adda mai suna Kachalla Ragas tare da wasu gungun ƴan ta’adda a wani hari da ta kai a ƙaramar hukumar Giwa dake Jihar Kaduna.

Kwamishinan sa-ido kan aikin jami’an na ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar da sanarwar, inda ya ce jami’an sun kai harin ne ƙarƙashin atsayen ‘Whiri Punch’ wanda ya yi sanadiyar mutuwar ƴan bindigan da dama ciki har da manyan kwamandojinsu a yankin ƙauyen Bula dake dajin Yadi a ƙaramar hukumar.

Yayin miƙa rahoton ga gwamnatin Jihar, Samuel ya ce jami’an sun yi nasarar hakan ne a lokacin da ƴan bindigan suka nufi yankin domin kai wani mummunan hari a kan baburansu, a inda jin hakan ke da wuya, sai jami’an suka far musu tare da hallaka da dama daga cikinsu.

A lokacin da yake magana kan lamarin, gwamnan Jihar, Uba Sani ya jinjina tare da yaba ma rundunar kan ƙoƙarinta na mayar da harin kan ƴan ta’addan da kuma nasara da ta samu.

Gwamnan ya kuma yi godiya ga waɗanda suka bada bayanan sirri da ma rundunar kan nasarar da aka samu bayan aukuwar lamarin.

Aruwan ya ƙara da cewa, ƴan ƙasa su cigaba da bada haɗin kai wajen basu bayanai da zasu taimaka musu wajen tabbatar da tsaro ta lambobi kamar haka; 09034000060 da kuma 08170189999.

By Babaji