Ba mu da ƙarancin ma’aikata da kayan aiki a asibitin ƙwararru na Gombe – Daraktan asibitin 

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Asibiitn ƙwararru na jihar Gombe shi ne mafi daɗewar asibiti a fadar jihar da aka gina shi tun kafin samun ‘yancin kan Nijeriya a shekarar 1958, kuma asibitin ya samu canje-canje sosai domin an fara shi ne tun daga matakin dispensary, ya koma cibiyar lafiyar matakin farko Primary Health Center, daga baya ya zama General sannan aka mayar da shi asibitin ƙwararru wato Specialist.

Jin ana kukan cewa asibitin yana fama da ƙarancin kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata, wakilinmu ya ziyarci asibiti inda ya zanta da Daraktan Asibitin Dokta Mu’azu Shu’aibu Ishaƙa, don jin irin halin da asibitin yake ciki.

Dokta Mu’azu ya ce ba su da ƙarancin kayan aiki da ƙwararrun likitoci sai ma ƙari da suka samu domin asibitin bai taɓa samun yawan ƙwararrun jami’ai da kayan aiki irin na wannan lokacin da aka gina asibitin.

Ya ce yawan da aka yi wa asibitin ne ya sa wasu suke ganin cewa akwai ƙarancin ma’aikata ko kayan aiki ko magunguna domin a cewarsa majinyatan da suke zuwa asibitin ba iya ‘yan Gombe kaɗai ba ne, kuma yanzu haka asibitin yana da ƙwararrun likitoci wato consultants guda 15 wanda a baya babu suna da kuma ƙwararru da suke zuwa ziyarar aiki sama da guda 10.

Daraktan ya ce suna da sababbin wuraren gwaje-gwaje na wankin ƙoda da na rage tumbi da sauran su na zamani wanda duka a wannan lokaci ne gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya samar da su bayan gyarar fuska da aka yi wa asibitin.

Ya ce jama’ar da suke zuwa jinya a asibiitn sun fi na baya shi ya sa ake ganin kamar suna da ƙarancin kayan aiki domin a shekarun baya har zuwa shekarar 2019 suna iya ganin majinta da basu wuce dubu goma sha uku bane a wata amma yanzu a kowanne wata daga 2019 zuwa 2024 suna ganin aƙalla majinyata dubu goma sha takwas.

Sannan a ɓangaren magunguna ya ce ba su da matsala domin gwamnatin jihar Gombe ta yi haɗin guiwa da wata hukuma ta GODMA da take zuwa har inda ake harhaɗa magungunan suna magana kai tsaye ana kuma samar da maganin da sauƙi, sannan kuma an shigar da mutane da dama tsarin jinya na adashen gata wato Go health inda suke kashe kuɗi kaɗan a lokacin jinya.

Daga nan sai ya ce duk magungunan da ake samun su da wahala zuwan wannan hukuma ya sauwaƙe musu suna samuwa da sauƙi don haka yanzu asibitin ba su da matsalar magani ko na ƙarancin likitoci.

By ukarofi