Sarkin Gona ya yi kira ga gwamnati da masu kuɗi wajen taimakon masu ƙaramin ƙarfi

Spread the love

Daga Abubakar A Bolari, a Gombe

Mai martaba Sarkin Gona da ke yankin Ƙaramar Hukumar Akko a jihar Gombe, Alhaji Umar Abdulkadir Abdussalam, ya yi kira ga gwamanti da masu hannu da shuni da cewa a dinga taimakon masu ƙaranin ƙarfi ganin cewa rayuwa ta yi tsanani.

Sarkin Gona, ya ce taimako ya yi ƙarancin al’umma na cikin matsin rayuwa hakan tasa  matasa masu tasowa ke zama barazana a cikin al’umma.

Mai martaba ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar sa inda yace dole sai gwamanti ta tashi tsaye tayi abunda ya dace akan matasan nan an samar musu da sana’ar da za su dogara da  ita dan ganin basu zama batagari ba.

Ya ce rashin aikin shi ke jefa  matasan ga halaka wajen shiga ayyukan ta’addanci da ke zama barazana  ga al’umma domin muddin matasan nan basu nitsu ba ba yadda za’ayi al’umma su samu zama lafiya.

A matsayinsa na uban ƙasa ya nemi gwamnati ta duba ta yadda za ta samarwa da matasan aiki yi duk da ma dai gwamnati na kokari domin ta kowacce hanya tana kokarin ganin ta samar musu da aiki saboda su dogara da kan su kamar yadda a wani shiri na samar da tsaro da kiyaye hatsura akan hanyoyi na GOSTEC aka dauki matasa dari biyar lokakci daya.

Ya yi amfani da damar wajen yin kira da cewa kowa ya ji tsoron Allah wajen yin abunda yake dai dai domin rashin taimako yanzu yayi yawa inda hakan ne yasa zakaga mutane sun zama mabarata  idan ba’a taikama musu ba suke kara zama nakasassu saboda rayuwar tayi tsanani kuma babu yadda suka iya sai sunyi bara sannan su samu abunda za su ci.

Mai martaba ya kuma koka kan yadda fyade ya yawaita da har ta kai ana samu wasu marasa kishi da kan iya amfani da irin ‘ya’yan da ake haifa ta wannan hanyar ake hada baki da wasu marasa kishi ake sayar da Yaran.

Ya ce irin wannan abun takaici shi ne ya jawo wani lokaci can baya a yankin masarautar sa a unguwar Barunde Yan sanda suka kama wata Mata ta hada kai da yan Social Welfare tana karbar irin wadannan ‘Ya’ya da ake haifa tana sayar da su a kudancin kasar nan

Lamido Gona, ya yi amfani da wannan damar inda ya yi kira ga masu hannu da shuni da cewa a dinga taimakawa mata gwabraye da zawarawa da marasa galihu domin akwai masu mazaje ma amma karfin mazajen ya kare wasu sunyi ritaya a aikin gwamnati ba Fansion ba Giratuti ba kuma abunda za’a ci a gida wanda hakan ya zama musu dole sai sunyi bara,

Ya ce rashin samun yadda za su ne ta ke kai wa wasu ‘ya’yan Mata suke bin samari dan samun kudi su bada kan su suna daukar dawainiyar iyayen nasu wanda kuma gaskiya hakan ba abu ne da ya dace ba.

Sannan sai ya jawo hankalin hukumomi da cewa su ci gaba da sanya ido a lungu da sako dan ganin ana zaƙulo irin wadannan batagari ana hukunta su dan barin su a cikin al’umma babbar masifa ce.

By ukarofi