Kotu ta bada umurnin riƙo na din-din-din ga kadarorin naira biliyan 12 da ke da alaƙa da Emefiele

Spread the love

Daga Sadiq Muhammad

Wata babbar kotun tarayya dake Jihar Legas, ta jaddada cewa, za a cigaba da riƙe kadarorin gwamnatin tarayya da aka ƙwace a hannun tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele waɗanda adadinsu ya kai sama da naira biliyan goma sha biyu.

Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke, ya yi hukuncin biyo bayan da wani jami’in hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa da laifukan da suka shafi kuɗi (EFCC), Chineye Okezie ya shigar da ƙara, inda ya ce a shari’ar karo na ƙarshe, za cigaba da riƙe kadarorin na din-din-din.

A ranar 5 ga watan Yuni, 2024 ne aka sanar da riƙe kadarorin na wucin-gadi wanda wani babban masanin Shari’a, Rotimi Oyedepo ya shigar da ƙara a kai inda ya sanar da kotun cewa bincike da nuna cewa Emefiele ya mallaki kadarorin ne ba bisa ka’ida ba tare da almundahana.

A ɗaya ɓangaren, hukumar EFCC ta bayyana sunayen mutane biyu da ake zargi da hanu a cikin lamarin da suka haɗa da Obayemi Oluawaseun Teben da kuma Akomolafe Adebayo waɗanda ke aiki da wani tsohon ma’aikacin CBN mai suna Olubunmi Makinde.

Mafi yawancin kadarorin an same su ne a ɓoyayyun yankunan Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

By Babaji