An kashe jami’an tsaro biyu a rikicin siyasar Ribas

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An kashe aƙalla mutum biyu a Jihar Ribas lokacin da wasu matasa suka mamaye gine-gine hedikwatar Ƙananan Hukumomi da dama, bayan da wa’adin shugabannin ƙananan hukumomin jihar 23 ya ƙare.

Lamarin ya faru ne a jiya Talata, bayan da gwamnan jihar, Siminialayi Fubara, ya umarci shugabannin sassan mulki na ƙananan hukumomin su karɓi ragamar tafiyar da ƙananan hukumomin.

Tun a ranar Litinin aka shiga zaman ɗar-ɗar bayan da wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin suka lashi takobin cigaba da zama a ofis, bisa dalilin cewa ’yan majalisar dokokin jihar 27 da ke rikici da gwamnan, waɗanda suke biyayya ga Wike sun yi wa dokar wa’adinsu kwaskwarima, ta yadda za su cigaba da zama a muƙamansu har wata shida bayan wa’adinsu.

Duk da cewa babbar kotun jihar ta yi gyara a kan dokar, wasu daga cikin shugabannin sun lashi takobin cigaba da zama a kan shugabancin lamarin da ya haifar da rikicin.

Da ya ke mayar da martani kan lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen, ɗaya daga cikin manyan dattawan jihar, Chief Edwin Clark, ya ɗora alhakin rikicin a kan tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja a yanzu Nyesom Wike, yana mai cewa dole ne a daina siyasar ubangida a jihar ta Ribas.

Jaridar vanguard wadda ta ruwaito labarin ta tabbatar da kisan wani ɗan sanda da kuma wani ɗan sa-kai na ƙungiyar ’yan sintiri.

Haka ita ma rundunar ’yan sanda ta jihar ta tabbatar da mutuwar mutum biyu sakamakon rikicin da aka gwabza tsakanin magoya bayan gwamnan da kuma tsohon ubangidan gwamnan na siyasa wato ministan na Abuja.

By ukarofi