APC ta buƙaci Tinubu ya saka dokar ta-ɓaci a Ribas

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta sake yin kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya saka dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin siyasar da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.

Jam’iyyar ta buƙaci da a tura sojoji da makamai a girke su a wurare na musamman a jihar domin kare abin da ta kira ɓarkewar rikici.

An ruwaito cewa shugaban riƙo na jam’iyyar a jihar, Chief Tony Okocha, shi ne ya yi kiran a ranar Laraba a wani taron manema labarai a babban birnin jihar, Fatakwal, yana mai cewa akwai lamau ƙarara na rashin bin doka da oda a jihar, wanda ya ce wasu da ba hukuma ba suna shiryawa.

Ya ƙara da cewa, idan ba a gaggauta ɗaukar matakin dakatar da yanayin ba, za a makara.

Okocha ya bayyana cewa dokar nan mai cike da taƙaddama (Law No 2 of 2024), wadda ’yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga ministan Abuja suka yi, ba sun yi ta ba ne da nufin tsawaita wa’adin shugabannin ƙananan hukumomin jihar da wa’adinsu ya ƙare ba, ya ce an yi ta ne saboda gaba.

By ukarofi