Sufeto Janar ya yi wa jami’ai da dama ƙarin girma

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A cikin makon nan ne Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya yi wa sabon mataimakin sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya DIG Yahaya Sahabo Abubakar ƙarin girma tare da mataimakan Sufeto Janar na ‘yan sanda tara, da liƙa wa kwamishinonin ‘yan sanda 15 sabbin muƙamansu a wani gagarumin biki da aka gudanar a ɗakin taro na Goodluck Ebele Jonathan da ke hedikwatar rundunar a Abuja.

Sabbin Mataimaka Sufeto Janar na ‘yan sandan da aka yi wa ƙarin girma sun haɗa da AIG Ahmed Ammani, Dankwara Adamu Mohammed, Mohammed Usaini Gumel, Adebola Ayinde Hamzat, fdc, Idegwu Basil Okuoma, Zachariah Fera Achinyan, fdc, Zango Ibrahim Baba, Isyaku Mohammed, da Margaret Agebe Ochalla.

A halin da ake ciki, akwai sabbin kwamishinonin ‘yan sandan da aka yi wa ƙarin girma kamar; CP Bassey Samuel Ewah, Osagie John Agans-Irabor, Edem Ita Selong, Monday Agbonika, fdc, Michael Okoh, Ayodele Oluyemi Sonubi, Iyamah Daniel Edobor, Isah Danladi Nda, Akaniyene Ifebem Ezima, Liɓingstein Ikioye Orutugu , fwc, mnips, Bello Rashid Afegbua, Hycenth Azuka Edozie, Haruna Alaba Yahaya, Peter Ozigi Umoru, and Ayotunde Godwin Omodeinde, mnips.

A cikin jawabinsa, IGP ya buƙaci sabbin jami’an da aka ƙara wa ƙarin girma da su nuna kwazo, sadaukarwa, da rashin son kai wajen gudanar da ayyukansu.

Ya yaba da kwazon da suka yi, wanda hakan ya sa suka samu wannan matsayi da suka cancanta.

IGP ɗin ya jaddada cewa sabbin muƙamai na nuna ƙarin nauyi da kuma amanar da aka ba su na cigaba da jagoranci ta hanyar misali ga ‘yan baya.

Haka zalika, DIG Dasuki Galadanchi, mni, an tura shi zuwa sashin leƙen asiri na rundunar, yayin da DIG Sahabo Abubakar aka tura ma’aikatar bincike da tsare-tsare, sannan aka tura AIG da CP zuwa ga sashn umarni da kafa rundunar.

Wasu daga cikin kwamishinonin ‘yan sandan da aka naɗa sun haɗa da CP Ayodele Oluyemi Sonubi zuwa rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, CP Dogo Salman na jihar Kano, da CP Bello Mohammed Sani na jihar Kebbi. Sauran sun haɗa da CP Adegbite A. Olaolu, MFR, zuwa INTERPOL FCID Abuja; CP Bassey Samuel Ewah zuwa Mataimakin Kwamandan Kwalejin ’Yan sanda; CP Iyamah Daniel Edobor zuwa Safer Highway DOPS FHƘ Abuja; CP Liɓinstein Ikioye Orutugu, fwc, mnips, zuwa Sashin Yaki da Ta’addanci FHƘ Abuja; CP Peter Ozigi Umoru, psc, mnips to Force Proɓost Marshall; CP Ayotunde Godwin Omodeinde, ya kai ziyara sashen damfara na ‘yan sanda na Legas; da CP Lanre Ogunlowo zuwa SIS/Shirye-shiryen Zabe, Kulawa da Kima, FHƘ Abuja, da sauransu.

IGP ya yi gargaɗin musamman game da duk wani yunƙuri na lalata tsarin tsarin girma a rundunar. Ya kuma jaddada muhimmancin riƙo da gaskiya a cikin rundunar, inda ya buƙaci masu waɗanda aka yi wa ƙarin girma da su yi jagoranci da jajircewa tare da kyakkyawan misali.

By ukarofi