Tare da ALI ABUBAKAR SADEEQ
Halifan Musulunci mafi shahara cikin jerin halifofin gidan Abbas (wato Abbasid ko muce Abasiyawa da hausa), wato Harun Al Rashid, ba’a taba samun mai kyauta irinsa ba. Shine halifan da kusan duk dare sai ya yi bad-da-kama ya shiga lungunan garin Bagadaza domin ganewa idonsa yadda talakawa ke rayuwa da zakulo mabukata domin tallafa musu. Rayuwarsa ce ta zama shahararren labarin nan na “Dare dubu da daya”.
Wata rana wani wazirinsa ya ce ya Amirul Muminun, ya aka yi kake da kyauta da karimci haka, sai ya dube shi ya ce “Kyauta ta zamto a cikin jinin jikina, yadda ko da a ce Allah ba ya bada Lada idan ka yi kyauta, to wallahi dadin da na ke ji yayin da na baiwa wani, wani abu, shi kadai ya ishe ni.”
Duk wanda ya tarbiyanyar da kansa da kyauta, wallahi zai gaya maka irin wannan nishadi da ruhi ke tsinkaya a yayin bada kyauta. Ta kan kasance mai kyauta na jin dadin kyautar da ya yi, fiye da wanda aka yiwa kyautar. Amma Kash! Kalilan cikin mutane ke iya tarbiyantar da kansu irin haka. Abubuwa biyu da shaidan ya sanya a gaba wajen cikar muradinsa na cewa;
Q15:29 “Ya Ubangijina Ina rantsuwa da abinda ka batar da ni da shi, hakika Ina kawata musu (rayuwa) a cikin kasa Kuma hakika Ina batar da su gaba daya.”
Su ne: Shirka da Rowa. Shirka ita ce ajandar shaidan ta farko wajen sutale bayi daga rahamar Allah, don haka shaidan ya lullube ta ta hanyoyi da ba zamu iya kauce mata ba sai mun yi da gaske, kamar yadda hadisin manzo ke cewa “Shirka za ta zama tamkar bakar tururuwa a kan bakin dutse, cikin duhun daren damina” kun ga sai fa wanda yayi sa’a ya zauna a kan wannan tururuwa ta cije shi zai iya ganewa ko? Da zarar ka yi Shirka, shi kenan Shaidan yayi maka rajista a kulob dinsa sai yayi gaba, domin baya neman komai kuma a wajenka.
Domin lalata rayuwar duniya Kuma, sai shaidan ya dauki makaminsa na rowa, ya assasa cikin rayuwar Dan Adam. Rowa, sabanin kyauta, ita ce ummul-aba-isun yawanci matsalar duniya. Ko tarihi ka duba, za ka ga cewa duk al’ummar da ta fi rarraba arzikinta tsakanin mutanenta ita ce a kowane zango na tarihi ta ke mulkar duniya.
A gaban idonmu yanzu haka, mu na kallo yadda Amurka ke mulkar duniya a yau saboda kokarinta na samar da arziki da yada shi tsakanin mutanenta. Kuma a idon namu mu ke ganin yadda China, da ta yunkuro a wannan fage na samar da arziki da yada shi tsakankanin al’ummarta, ga shi nan tana daf da buge Amurka ta karbe jagorancin duniya.
Shine hikimar da Allah ya wajabta zakka tsakanin al’ummar musulmi domin a rarraba arziki kowa ya amfana. Hatta ita zakkar, shaidan bai barta ba sai da ya cuso rowa cikinta yadda ba a iya bada ita yadda Allah ya umarta cewa;
Q6:141 “…Ku ci daga yayan itacensa, idan yayi yayan, Kuma ku bayar da zakkarsa a ranar girbinsa.”
Wato falsafar musulunci ita ce a yada arziki. Duk sanda Allah ya ni’imta ka sai ka ni’imta bayinsa, amma sai ga wata kullalliya cewa zakkar kudi sai sun shekara a ajiye sannan za a bada zakkarsu. Bayan ga Allah ya koya mana da kansa lokacin bada zakka (ranar duk da ka girbe ko ka sami riba). Allah ya gargadi masu boye dukiya su ki fitar da zakka cewa;
Q63:10 “Kuma ku ciyar daga abinda mu ka azurta ku daga gabanin mutuwa ta je wa dayanku har ya ce “Ubangijina don me baka yi min jinkiri zuwa wani ajali makusanci domin na gaskata kuma in kasance daga salihai.”
Wato ku gaggauta fitar da zakka lokacin da duk kuka sami nisabinta, wanda ya ce sai ta shekara a ajiye, yana da yakinin kaiwa badi? Idan kana da hisabin zakka yau ka ce sai badi zaka fitar, to sai ka mutu bayan wata uku, hakkin zakka na kanka amma dukiya ta zama gado. To irin wadannan su ne wadda aya ta sama ke wa gargadin cewa zasu ce Ina ma Allah yayi musu jinkiri da sun fidda zakka.
Yayin da al’umma ta yaki talauci, ta hanyar raba zakka ga ahalinta a kan lokaci, kuma kyauta ta yawaita tsakanin al’umma, wajibi kwakwalen mutanenta su yi aiki wajen kawo ci gaba da fadadar tattalin arziki. Idan kuma ta rungumi rowa da hadama, ta hanyar kin yin zakka, kyauta da sadaka, sai koma-baya da masifu iri-iri su mamaye ta kamar yadda muka sami kan mu a yau.
Kyauta kuma halayya ce da ke karfafa soyayya da dakile kiyayya tsakanin mutane. Amma sai shaidan ke hura mana wutar rowa cikin zukata, da barazana da talauci. Al’ummar arewacin Najeriya a yau, sun fada cikin bala’o’in duniya sakamakon hudubar rowa da shaidan ya yi mana. Yan bokon farko bayan su Sardauna sun assasa rowa cikin rayuwarsu yadda ta fantsama zuwa ga yan siyasa da ma sauran al’umma. Babbar illar rowa shine akasari kuma sai ta haifarwa mai ita hadama. Da zarar rowa ta hade da hadama, shi kenan bala’i ya tabbata. Abinda ke faruwa kenan a tsakaninmu yau a Arewa.
Kamar yadda Shirka ke rushe mutane a lahira, haka rowa ke rushe mu a doron kasa. Duk Wanda ka ga Allah ya wadata shi amma ya zama marowaci, to ka tausaya masa domin ya na daga cikin manyan alamomin yan wuta, kamar yadda Allah ya nuna mana cikin;
Q92:8-11 “Kuma amma wanda ya yi rowa, Kuma ya wadatu da kansa…zamu saukake masa har ya kai ga tsanani, Kuma dukiyarsa ba za ta wadatar masa da komai ba, a lokacin da ya gangara wuta.”
Ana tarbiyantar da ruhi wajen yin kyauta tun daga yarinta, shi yasa wajibi al’umma ta rika koyawa yara kyauta tun suna kanana, sannu a hankali har mutum ya kai matsayi irin na su Harun Al Rashid, wato ko babu Lada, farin cikin da ke mamaye mai kyauta idan ya taimaki wani ta ishe shi. Shi ko mai rowa, azabar ruhi ya ke kamuwa da ita, domin duk sanda ya yi rowar, sai ya yi ta kokawa da “Nafsin lawwamah” wato zuciyarsa ta yi ta zargin kansa da kansa.
A wannan yanayi na sallah babba, Musulunci na kokarin koyawa mutane yin kyauta ne. Amma idan ka kalli yadda a zahirance mu ke aiwatar da abubuwa sai ka gane cewa shaidan ya musanya mana tsarin na kyauta ya koma rowa. Misali a baya zaka ga ana kulla nama a rabawa makwabta, yanzu fa? Sannan a da, za ka ga attajirai na rabawa talakawa raguna amma yanzu sai kaga an maida abin kamar cin hanci, yadda yan siyasa kan siya su rabawa magoya baya, Sarakuna da ma’aikata. Muna yara sai ku wuni ranar sallah ku na kai abinci makwabta da unguwa unguwa. Amma yanzu makwabcinka ma baka san me ya dafa ba shi ma bai san me ka dafa ba. Rowa ta maye gurbin kyauta an koma sai cece-kuce kan halasci ko akasin haka kan azumin Arfa.
A karshe mu fahimci cewa Babbar alamar yan aljanna ita ce kyauta, haka nan babbar alamar yan wuta ita ce rowa. Domin duk wanda Allah ba ya so da rahama shine yake wadata shi, kuma ya hane shi yin kyauta. Allah ya kiyashe mu.
Sannan kuma kada mu manta;
Q47:38 “…Kuma wanda ke yin rowa, to, ya na yin rowar ne ga kansa.”
Don haka kada ka ji haushin marowaci ko kadan, kansa ya zalunta ba wadanda ya yiwa rowar ba.
BARKAN MU DA SALLAH BABBA, ALLAH YA MAIMAITA MANA MALAMAI!
Ali manazarci ne, wanda kuma ya rubuto daga Kano
