Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu matasa shida sun nutse a kogin Mbang da ke kusa da ƙauyen Ribang (Mbang) a Ƙaramar Hukumar Kauru a jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa, matasan sun nutse ne a lokacin da suke dawowa daga jarrabawar kammala aji uku ta ƙaramar sakandare da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga watan Yuni, 2024.
Waɗanda suka mutum sun haɗa da Manasseh Monday (mai shekara 16), Musa John (shekara 16), Pius Daɓid (shekara 15), Monday Ayuba (shekara 16), Daɓid Danlami (shekara 19), da Yahuza Audu (shekara 16) ɗaliban makarantar sakandaren gwamnati ta Fadan Chawai suna rubuta Jarabawar JSCE
Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar raya Ribang, Fasto Simon Ishaku, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Laraba.
Ishaku ya ce tuni aka gano gawarwaki uku tare da binne su.
Ya ƙara da cewa har yanzu akwai uku da suka ɓata saboda mutanen yankin sun kasa gano su daga cikin kogin.
Ishaku ya ce, “Yaran ‘yan makarantar sun bar gidajensu cike da bege da annashuwa yayin da iyayensu suka je gona da fatan haɗuwa da su bayan sun rubuta takardan ranar, sai suka gamu da ajalinsu.
“Kogin Mbang ya kasance tarkon mutuwa ga mutanenmu tsawon shekaru, lura da cewa kafin al’umma su iya shiga kowace makaranta ko duk wani asibitin da za su yi tafiya na kimanin kilomita 8.
“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya, Gwamna Uba Sani, Sanata Sunday Katung da ’yan Majalisar Wakilai da su taimaka mana da makarantu, asibitoci, hanyoyin shiga da gada domin kawo wa al’ummarmu taimako. , inji Ishaku.
Har yanzu jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin.
Amma kodinetan shiyyar na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna shiyya ta ɗaya Mubarak Muhammad ya ce zai tabbatar da faruwar lamarin tare da sanar da jama’a a hukumance.
