‘Yan bindiga sun ƙi sakin ƴaƴan alƙalin da aka sace a Kaduna bayan sun sako ta

Spread the love

Daga BALA MUHAMMAD

An sako Alƙalin da aka yi garkuwa da ita tare da ‘ya’yanta huɗu a Kaduna, Janet Gimba a watan da ya gabata.

Sai dai ƴaƴanta uku har yanzu ba su dawo gida ba kamar yadda mijinta, Musa Gimba ya tabbatar.

Ya ce, ƴan bindigar suna gargaɗin cewa a biya Naira miliyan 150 nan da kwana uku ko kuma su kashe su.

A ranar 24 ga watan Yuni, 2024 ne aka yi garkuwa da matar wacce ke aiki a reshen Sabon Tasha na babbar kotun jiha tare da ƴaƴanta huɗu a gidansu da ke yankin Mahuta a ƙaramar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar Ƴan sandan Jihar, Mansir Hassan ya ce daga baya ƴan bindigar sun kashe babban ɗan matar, Victor Gimba mai shekaru 14 inda ya ce an samu gawarsa a Sabon Tasha, a unguwar Bayero na Ƙauyen Dutse a bakin babbar hanyar Kaduna-Abuja a ranar 2 ga watan Yuli.

Mansir, ya ƙara da cewa suna aiki tuƙuru tare da wasu hukumomin tsaro wajen ganin an ceto yaran daga hannun ƴan bindigar.

By Babaji