Dole masu POS su yi rijista kafin ƙarewar wa’adi – Hukumar CAC

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gabanin cikar wa’adin yin rajistar kasuwanci na dole tare da Hukumar Kula da Kamfanoni ta Nijeriya, CAC, Jakadan Hukumar, Michael Nwabufo, ya buƙaci masu sana’ar POS da masu ƙananan sana’o’i su gaggauta yin rajista da hukumar.

Nwabufo, manajan tallar hukumar, ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar kwanan nan a Legas cewa dole ne masu POS su guje wa rikice-rikice ta hanyar tabbatar da rajistar su kafin wa’adin.

Da yake ƙarin haske kan mihimmancin wa’adin, wanda ya rage saura kwanaki biyar, Nwabufo ya ƙarfafa ‘yan kasuwa da su yi amfani da manhajar CAC Special Registration Portal (SRP) don yin rajista.

“Wannan shiri wani muhimmin ci gaba ne, wanda ya samar da tsarin yin rajista mai inganci kuma mai amfani ga dukkan ‘yan Nijeriya. Muna ƙarfafa ƙananan ‘yan kasuwa, musamman ma’aikatan tallace-tallace, don yin rajista ta hanyar SRP. Wannan rajista na yau da kullun ba wai kawai yana ba da amincewar doka ba har ma yana haɓaka sahihanci kuma yana buɗe damar cigaba,” inji shi.

Ya yi nuni da cewa dandalin PCCSIGN yana bada tsarin rajista wanda ya dace da buƙatun al’umma, kuma yana ba da ƙarin hanyar yin rajista cikin sauri da inganci.

By ukarofi