EFCC ta tsaurara tsaro a Abuja, Legas da Ibadan bisa shirin yi wa hukumar zanga-zanga

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC), ta ɗauki matakin tsaurara tsaro a ofisoshinta da ke Abuja, Lagas da Ibadan, babban birnin jihar Oyo, biyo bayan raɗe-raɗin cewa an shirya za a yi mata zanga-zanga a ranar juma’a 5 ga watan Yuli.

Jaridar ‘The Nation’ ta ruwaito cewa, a jihar Legas, an sanya wasu jami’an hukumar tare da ‘Yan sandan farin kaya na DSS a dukkan hanyoyin da za su kai zuwa ofishinta da ke hanyar Awolowo a ƙaramar hukumar Ikoyi.

Haka nan a jihar Oyo, wani mai suna Steve ya sanya a shafinsa na ‘Twitter’, @Foreman123 cewa “an baza jami’ai a zagayen ofishin hukumar da ke Iyaganku GRA – kamar gwamnati ta ankara, kar a maimaita abin da ya faru a lokacin zanga-zangar ‘EndSars’ ” inji shi.

Wasu ƴan Nijeriya sun shirya zanga-zangar da su ka kira da ‘ReformEFCC’ wanda a ke fakewa da ita wajen cutar da waɗanda basu ji ba basu gani ba, inda hukumar ta hasato wani tsohon gwamna da wasu tsoffin ministoci biyu da ɗaukar nauyin haka.

Rahotanni sun nuna cewa, za a gudanar da zanga-zangar a jihohin Edo da Kwara da Gombe da Enugu da Abuja da dai sauransu.

By Babaji