Sarki Sanusi ya yaba wa Gwamnan Kano bisa bai wa ‘yan fansho da ilimin yara mata muhimmanci

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya jinjina wa gwamna Abba Kabir Yusuf kan warware matsalolin biyan ƙuɗaden fansho da kuma bada muhimmanci ga ilimin yara mata.

Sanusi ya yi hakan ne la’akari da yadda mutane da dama suka shiga matsanancin rayuwa da talauci wanda rashin biyan su kuɗaɗensu na fansho da giratuti ya zama dalilin samun kansu a wannan hali.

A kwanakin baya ne, gwamnan ya sa a ka ware Naira biliyan 11 domin biyan waɗanda ke karɓar kuɗin fansho ciki har da waɗanda aka riƙe mu su na tsawon lokaci, inda Sarkin ya yaba masa, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen fitar da su halin ƙuncin da su ke fuskanta.

Sannan, Sarkin ya yi tsokaci kan yadda gwamnan ke ƙoƙari wajen bunƙasa ilimin yara mata, inda a yayin wata hira a fadarsa da kwamishinan labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye da takwaransa na kimiyya da fasaha, Alhaji Mohammed Tajo, ya ce an samar da motocin zirga-zirga da kayan koyarwa ga malamai da ɗaliban makarantu.

Mai martaba Sanusi ya ƙara da cewa, ilimin yara mata abu ne da zai taimaka wajen warware matsalolin auren wuri da haihuwa da kula da yanayin cin abinci da kuma talauci.

Kazalika, ya yi kira ga ma’aikatu masu zaman kansu da su bai wa gwamnatin haɗin kai a ƙoƙarinsa na gina makarantu da samar da kayan sufuri ga ɗalibai da kuma shirin ciyar da su abinci.

By Babaji