Gwamnatin Tarayya ta dakatar jirage masu zaman kansu 10

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar kula da harkokin jirage masu zaman kansu (NCAA), ta dakatar da zirga-zirga da ayyukan wasu jirage guda 10 biyo bayan da su ka gaza sabonta tantancewarsu daga gare ta.

Wata sanarwa da NCAA ta saka a shafinta na ‘Twitter’ wanda ke ɗauke da sa hannun daraktanta kan hulɗa da jama’a da kula da abokan hulɗa, Micheal Achimugu, ta ce ta bayar da umarni ga waɗanda ke mallakan jirage domin amfanin kansu da su sake zuwa a tantance su wanda wa’adin hakan ya kamata a ce ya ƙare tun ranar 19 ga watan Afrilu, 2024.

Achimugu ya ce, sun yi hakan ne saboda masu gudanar da jiragen su saɓa ma dokar hukumar da ta umarci dukkan masu aiki da jiragen gida, kada su yi amfani da su wajen harkar kasuwanci kamar abin da ya shafi ɗaukar fasinja, kaya ko bayar da haya da makamantansu.

A sakamakon haka, hukumar ta fitar da sanarwar dakatar da zirga-zirgan jirage kamar haka; Azikel Dredging Nigeria Ltd; Bil-Aviation Safety Service; Worldwide SkyPaths service; Mattini Airline Services Ltd; Aero Lead Ltd; Sky Bird Air Ltd; da kuma Ezuma Jets Ltd.

NCAA ta ƙara da kira ga jama’a, da su guji hulɗa da su, domin duk wanda aka samu cikin haka, to doka za ta yi aiki a kansa.

By Babaji