
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wani ɓangare na majalisar dokokin jihar Ribas ƙarƙashin jagoranci Vickto Oko-Jumbo ya ce ba su amince da hukuncin kotun ɗaukaka kara ba biyo bayan sanar da Martins Amaewhule a matsayin halstaccen kakakin majalisar.
Oko-Jumbo wanda shi ɗan bangaren gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ne ya faɗi hakan a yayin wani zaman majalisar a Fatakwal, babban birnin jihar.
A ranar Alhamis ne kotun ta yi watsi da hukuncin babbar kotun jihar wacce ta sanar cewa Amaewhule da wasu ƴan majalisu 24 ba sa cikin mambobin majalisar dokokin jihar.
Kotun ɗaukaka ƙarar, ta ce babbar kotun jihar ba ta da ikon shiga lamarin da ya shafi sauya sheƙa da ƴan majalisu ke yi, sai dai, Oko-Jumbo ya ce majalisar ta ce faɗar hakan kuskure ne a gare ta.
Oko-Jumbo, ya ƙara da cewa, “har yanzu ni ne halastaccen kakakin majalisar, kuma bai yiyuwa a samu shuwagabanni biyu a majalisar kowace jiha kuwa, ko Ribas ce” inji shi.
Kazalika, ya ce tsohon kakakin majalisar ya sanara da sauke Amaewhule da wasu 24 daga muƙamansu kasancewar sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a watan Disambar 2023.
Sannan, ya ce sun samu takardar umarnin kange Amaewhule da ƴan ɓangarensa daga ikirarin su mambobin majalisar ne.
