Alƙalan babban kotun Kano sun ƙalubalanci cire su daga hukumar shari’a ta binciken Ganduje

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Alƙalan babbar kotun kano sun ƙalubalanci cire su daga hukumar shari’a ta binciken tsohon gwamnan kano Ganduje. Waɗannan hukumonin shari’ar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya kafa su domin suyi wannan aiki.

Mai shari’a Farouk da mai Shari’a Zuwaira an naɗasu su shugabanci waɗanda hukumomin domin bincikar almundahana, rikicin siyasa, mutanen da suka ɓace da kuma shekara takwas na tsohon Gwamna Ganduje.

Sai dai ana tsaka da haka, sai babbar kotu ta ƙasa a karkashin mai shari’a Simon Amobeda ya bada hukuncin dole su sauka daga wannan kujeru cikin awa 48, ko su rasa wasu alawus da alfarmar daga kungiyoyin alƙalai ta ƙasa.

Saboda haka ne, Alƙalan biyu tare da kwamishinan shari’a na jihar kano, suka ɗaukaka ƙara.

By ukarofi