Daga MUHAMMADU MUJJITTABA a Kano
Hon. Yusuf Imam Ogan Ɓoye, mai bai wa gwamna shawara kan harkokin matasa da wasanni na jihar Kano, ya jagoranci ƙaddamar da wani littafi da akai wa take da ‘Abin Cikin Ƙwai’ da Bahaushe ya ce ya fi ƙwai daɗi, a wani taro da ƙungiyar marubuta ta kafofin sadarwa ta zamani ta gabatar a ranar Lahadi da ta gabata a birnin Kano.
A jawabinsa Amb Yusuf Ogan Ɓoye wanda kuma aka karramashi a taron ƙungiyar ya nuna gamsuwarsa da yadda taron ya kasance inda kuma ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana irin ƙudurori na ciyar da matasan Kano gaba domin samar da kyawawan shugabanni na gabata a matsayinsa na jagora wanda ke tare da matasa tun kafin wannan muƙami na matasa da gwamnatin kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf ga wannan muƙami na mai bawa gwamna shawara a kan harkokin matasa da wasanni na Kano.
Shi ma a jawabinsa Amb Ado Ahmad Gidan Dabino MON Sarkin Mawallafin Arewa, ya bayyana cewa wannan taro nya samu kyakkyawan nasara ganin yadda aka yi lafiya aka tashi lafiya, kuma ya samu halattar fitattun marubuta a wannan taro da mawallafa waƙoƙi, irin su Dr. Aminu Ladan Abubakar ALA, Sarkin Ɗiyan Gobir, Ɗan Amanar Bichi Sarkin Waƙar Dutse, da sauran waɗanda aka gayyata irin su Bilkisu Yusuf Ali da sauran masana daga jami’o’I da cibiyoyin ilimi.
A ƙarshe an karrama wasu fitattun mutane dangane da gudummawar da su ke bai wa wannan ƙungiya marubuta online a taron ta karo na farko da aka yi a Kano.
