Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan sanda sun kama shugaban ’yan banga da ƙoƙon kai biyu da wasu sassan jikin dam Adam a Jihar Ribas.
Rundunar ’yan sandan jihar ta bayyana cewa dubun Feliɗ Nwaobakata ta cika ne a yayin aikin samamen da ta ƙaddamar domin magance wuce gona da iri da ’yan banga ke yi a jihar.
Feliɗ Nwaobakata da aka samu da sassan jikin ɗan Adam a maboyarsa da ke yankin Omoku da ke a Ƙaramar Hukumar Ogba-Egbema-Ndoni shi ne shugaban ƙungiyar ’yan banga ta ONELA (OSPAC) a yankin.
Kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko, ta ce an kama wasu mambobin OSPAC bakwai kan zargin aikata kisa da wasu manyan laifuka.
Ya bayyana cewa Nwaobakata shi ne babban wanda ake zargi a kisan wasu mutane biyu ’yan uwan juna a yankin Idu bisa zargin su da laifin garkuwa da mutane a ranar 1 ga watan Mayu, 2024.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin taka wa ’yan bangar burki ne sakamakon korafe-korafen jama’a kan yadda suke cin karensu babu babbaka a jihar.
Jami’in ya ce a kwanakin baya ’yan bangar OSPAC sun kai hari Babban Ofishin ’Yan Sanda na yankin Omoku, baya ga fito-na-fito da suke yawan yi da jami’an tsaro a sassan jihar.
“Rana 9 ga watan Mayun 2024 Sarkin Hausawa a yankin ONELGA, Alhaji Usman Seleh, ya kawo kara cewa ’yan OSPAC sun yi garkuwa da wani mutum a cikin al’ummarsa.
“Sakamakon haka ’yan sanda suka gayyaci shugaban ONELGA OSPAC, Feliɗ Nwaobakata, amma ya ki zuwa.
“Maimakon haka, sai ƙungiyar OSPAC ta kai hari Babban Ofishin ’Yan Sanda na Omoku, amma jami’an da ke ofishin suka fatattake su.
“Bayan nan ne aka kai samame a cibiyar kungiyar da ke Omoku inda muka kama bakwai daga cikin mambobin.
“Daga bisani muka kama shugaban ONELGA OSPAC, Feliɗ Nwaobakata, a ranar 17 ga Yuni, 2023, inda muka same shi da kokon kai guda biyu da kasusuwa da wasu sassan jikin dan Adam.
