Mun gamsu da yadda Gwamna Abba ke gina ci gaban Jihar Kano a tsarin Kwankwasiyya – Musa Gambo Ɗanzaki 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana shekara ɗaya da rantsar da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf  irin ayyuka da ya gudanar a zahiri  sun fi na shekaru takwas da tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

Shugaban Kwankwasiyya na Jihar Kano, Hon. Musa Gambo Hamisu Ɗanzaki ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce sun gode wa Allah da jinjina ga jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso bisa hangen nesa da ya yi na zaɓo musu jajirtacce, haziƙin Gwamna Abba Kabir Yusuf domin irin ayyuka da yake bijirowa dasu kwalliya ta na biyan kuɗin sabulu.

Ya ƙara da bayanin cewa abubuwa da yawa sun faru na cigaba  da a baya an daƙile su a  Jihar Kano da zuwan Gwamna Abba ya farfaɗo da Jihar Kano  daga halinda aka jefa ta a ciki. Daga  zuwansa ya ɗauki mataki na ganin an  inganta tsaro ta kauda matsalar daba da kwacen waya da ya addabi mutane.

Haka a ɓangaren kula da lafiya ya farfaɗo da Asibitoci da suke Kano ta yi musu gyara da samar da kayan aiki, al’umma shaida ne akan abinda ya faru ga Asibitin Asiya Bayero Gwamna ya karɓo shi ya inganta shi aka samar da kayan aiki akayi masa gyara ya dawo cikin hayyacinsa ana aiki kula da lafiya kowane lokaci.

Haka a ɓangaren Ilimi ya tura ɗalibai 1001 waje karatu ya dawo da wasu makarantu  da aka rufe guda 25 da suka haɗa da na koyon kiwon kifi dana  koyon sana’oi dana fasahar sadarwa  da sauransu duk  domin cigaban al’ummar Kano.Sannan ya  gyara albashin  ma’aikata wanda   a baya basu  san takamaimai abinda ake biyansu ba  saboda yanke musu  da ake  a Gwamnatin Ganduje. Yanzu kuwa suna samun cikakken  albashi   da  biyansu  akan kari tun daga 25 ga wata wannan ba ƙaramin namijin ƙoƙari bane na Gwamnan.

Shugaban Kwankwasiyya na Jihar Kano, Hon. Musa Gambo Hamisu Ɗanzaki ya ce a fannin inganta noma Gwamna ya ɗauki matakai na tallafawa manoma da taki.da iri.Aka dawo da tsarin baiwa Mata jari duk wata Mata guda 100 a dukkan kananan hukumomi 44 ana baiwa kowace mace  jarin N50,000. Haka ya zo ya kalli yan fansho da a shekara takwas na Gwamnatin Ganduje ba a taɓa biyansu haƙƙinsu na garatuti da zuwan Abba ya ware Naira biliyan 11 ya soma  biyan su  tareda ƙarawa yan Fansho  albashi suna godiya ga Allah da ya dawo da Gwamnatinsu ta tsarin Kwankwasiyya a Jihar Kano.

Hon. Musa Gambo ya ƙara da cewa duk ƙasar nan ba wani Gwamna da ya iya ware biliyoyin  kuɗi ya biya yan fansho idan ba Abba Kabir Yusuf ba, sannan gashi ana gudanar da aikin manyan hanyoyi  na gadojin ƙasa da sama a Tal’udu da Ɗan’agundi da Kuma  cigaba da aikin hanyoyi na kilomita Biyar-biyar da aka soma a lokacin Kwankwaso da  Ganduje ya zo ya ƙi aiwatarwa. Yanzu haka akwai aikin Gina rukunin ajujuwa na makarantun furamare bene mai hawa biyu a dukkan ƙananan hukumomi 44 da za ayi.

Ya yi nuni da cewa shi Gwamna Abba Kabir Yusuf jajirtacce ne tun rantsar dashi yake aiki tuƙuru  hatta shari’a da aka keto na zaɓe bai sa ya yi sakaci da gudanar da aiki ba kullum a ziyarar aiki yake wannan ya nuna shi gwarzo ne duk Wanda ya sanshi dama a  lokacinda yake kwamishina a lokacin Kwankwaso ya sanshi da tsayuwar daka akan kula da aikace aikace na al’umma da hakkinsu.

Ya ce da ikon Allah a lokacinda Abba zai cika  Shekara ta biyu akan mulki al’ummar Jihar Kano za suga cewa tabbas zaɓenda suka yi masa  za su ce anyi abinda yakamata kuma aikinsa zai shafe na sauran Gwamnoni saboda ya ɗauko aikace-aikacen alkhairi.Al’ummar Kano su cigaba da taya Gwamnan  da addu’a Àllah ya kama masa da yin riƙo da hannunsa ya bashi ikon sauke nauyi.

Shugaban na Kwankwasiyya na Jihar Kano.Hon.Musa Gambo  ya ce kullum tafiyar Kwankwasiyya sai  ƙara karɓuwa da farin jini take a Nijeriya har ma a wasu jihohin na kudu  suna yin  dana sanin rashin zaɓen Kwankwaso a zaɓen 2023 a matsayin shugaban ƙasa, domin sun san da shine ke mulkin ƙasar nan da ba’a sami kai a halinda ake ciki na wahalar rayuwa ba.

Ɗanzaki ya ce yana fata a zaɓe mai zuwa na gaba yan Nijeriya za su fito kwai da ƙwarƙwata don su zaɓi Kwankwaso a matsayin shugaban ƙasa.

Hon. Musa Gambo Hamisu Ɗanzaki shugaban Kwankwasiyya na Jihar Kano ya  jaddada  cewa suna nan akan bakansu daram  a matsayinsu na yan kwankwasiyya, jagoransu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso zai fito takarar shugaban ƙasa a 2027  da yardar Allah  don  haka ya ja hankalin  manya da  jagororin  Arewa su ajiye adawa ta siyasa  da ƙiyayya da  hassada da suke yi  masa, su zo su mara masa baya, domin kaiwa ga gaci domin shi Kwankwaso  cigaban al’umma  ne a gaban sa kawai  ba wani abu ba.

By ukarofi