Siyasa ke kawo tarnaƙi a yaƙi da ake da cin hanci da rashawa a Nijeriya – Ɗanpass

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano 

Ɗan Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ya bayyana cewa batun yaƙi da cin hanci da rashawa akwai siyasa a cikinsa.

Ya ce domin irin abinda yake faruwa a ƙasar nan sai mutum ya kwashi dukiyar al’umma, amma duk da hukumomi na yaƙin da almundahana irin su EFCC da ICPC suna kamawa amma idan aka kai ga matakin shari’a  sai a bada belinsu shi kenan sai aji shiru.

Ya ce in ana son gyara sai an tsaya an riƙe amana da gaskiya da tsoron Allah shine zai sa waɗannan  abubuwa za su tafi daidai a ƙasar nan.

Ya ce abubuwa da aka sani sai daɗa taɓarɓarwa suke kowa abinda ya ga dama yake. Shugabanni idan suna kan mulki sun zama za su kare muradinsu na son ransu ne, in suna kan kujerar mulki sun zama zakoki amma da sun sauka daga su sai na kusa da su.

Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ya ƙara da cewa ya kamata dai duk abinda za ayi ayi don Allah aji tsoron Allah sai a sami albarkar abin a kuma riƙa tuna mutuwa domin duk mai rai mamaci ne,amma basa tunanin wannan shi yasa ma za a ga tsoffafi dake mulki  ke  tsoron matasa su yi mulki, domin in matasa suna mulki za a sami cigaba a ƙasar nan, yanzu ga ƙasar Senegal matashi ne ke mulki ana kuma yabonsa.

Ya ce yanzu a Nijeriya mulki daga tsoffafi ‘yan shekaru sama da 70 sai sama da 80 da suke ɗuwada son ransu yaya za a yi abubuwa su tafi daidai.

Ya ce  lauyoyi da  shara’a da tsaro nasu ne sai abinda suka ga dama suke yi,amma da shari’a za ta sami gashin kanta da duk irin wannan ba za su faru ba.

Ɗanpass ya ce tun daga kan shugaban ƙasa da gwamnoni da  ministoc  da shugabannin hukumomi na gwamnati akwai sai abinda suka ga dama suke da kuɗin ƙasar nan.

Ya yi nuni da cewa ƙasa kamar Nijeriya ace sai an je an ciwo bashi a ƙasashen duniya alhali ba abinda ba mu da shi na arziƙin da albarkatun ƙasa, amma sai aka dagula al’amuran, muddin  ba gyara aka yi  ba, komai zai cigaba da zama matsala, dole a kawo gyara a rungumi matasa a ɗora su a hanya ta bunƙasa cigaban ƙasa don a samu zaman lafiya.

Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass ya ce abu ne mai kamar wuya a iya kauda matsalar cin hanci da rashawa cikin ƙananan lokaci sai an tashi an yi aiki da gaskiya da amana da kishin ƙasa a inganta  shari’a da tsaro sannan za a sami kyakkyawar mafita.

By ukarofi