Wani mutum da ba a san ko waye ba, ya haye ƙarfen sabis a Abuja, domin ya gaji da rayuwa saboda wahalar da ke ciki.
Wani ɗan ƙaramin jawabi da ya ajiye, ya na cewa, a dawo da tallafin man fetur da kuma sauran matakan domin rage raɗaɗin ga yan Najeriya. Ya cigaba da cewa a shirye yake ya sadaukar da rayuwar shi in har waɗannan abubuwan basu samu ba.
A cikin takardar ya cigaba da cewa, gwamnati ta ayyana dokar ta ɓaci a kan jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi, Sokoto da Niger saboda rashin tsaro.
Ya buƙaci gwamnati ta buɗe boda saboda a samu damar shigo da abinci.
A yayin wannan rahoton, hukumar da ke bada agajin gaggawa sun hallara wajen, tare da hukumar kashe gobara ta ƙasa.
