Shugaba Tinubu ya taya Sheik Ɗahiru Bauchi murnar cika shekaru 100 a duniya.
Ya bayyana Sheik Ɗahiru Bauchi a matsayin mutum wanda ya sadaukar da rayuwar shi wajen bada ilmi da kuma haskaka rayuwar al’umma..
Sanarwar ta fito daga bakin mai bada shugaban ƙasa shawara bangaren kafafen sadarwa. Yace, Shehin malamin mutum ne daya sadaukar da rayuwar shi wajen bada ilmi da kuma zama jagora nagari wajen matasa masu tasowa.
