Bishiyun shekara 100 sun faɗo sun kashe ƴan kasuwa huɗu a Edo

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wasu bishiyu uku a kasuwar Jattu dake ƙaramar hukumar Etsako ta yamma a jihar Edo, sun yi sanadiyar mutuwar mutum huɗu bayan da suka faɗo a kan ƴan shan inuwa da masu shaguna.

Wani adadi da ba a tantance ba na mutane sun samu raunuka a yayin aukuwar ibtila’in.

Blueprint ta ruwaito cewa yayinda ake ruwan sama da misalin ƙarfe takwas na safe, masu saye da sayarwa sun fake a ƙarƙashin rumfunan bishiyun inda aka yi wani tsawa da ya yi sanadiyar faɗuwarsu wanda a sakamakon haka ne aka rasa rayukan.

Wani mai suna Sule, ya faɗi cewa, bayan aukuwar lamarin ne aka garzaya da waɗanda suka ji raunuka asibiti yayinda aka kai mamatan gidan ajiyar gawawwaki.

Shugaban ƙaramar hukumar, Marvelous Zibiri ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce mutuwar mutanen abin alhini ne a gare su.

Ya kuma shawarci mutane da su daina fitowa waje yayin ruwan sama tare da jajentawa waɗanda al’amarin ya shafa.

Kazalika, ya ce za su gyara inda ibtila’in ya lalata tare da yanke duka bishiyun da ke kasuwar.

By Babaji