(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Idan ba mu manta ba, kuma kuna biye da jaridar Manhaja, a makon da ya gabata, mun ɗauko bayani kan kayan da ake kai gidan miji da ke da suna gara a al’adance.
Mun faro bayanin kan irin kallon da ma’anar da take da shi a tsakanin al’ummarmu, musamman ma a Ƙasar Hausa. Inda muka yi bayanin yadda muhimmancin ta ke rasiri a zamantakewar aure a wasu lokuta.
Mun yi bayanin yadda barin ta yafi zama alheri da wasu hujjojin da muka kawo, kafin mu ja birki da tambayar da na san da yawa suna yi wa kansu ita, wato ko gara na da matsuguni a Musulunci?
Akwai wani masanin tarihi da ya yi wani dogon bayani kan abinda ya shafi gara, inda a zantukan nasa ya tabbatar da samuwar wani abu mai kama da gara a zamanin magabata. A cewarsa, a lokacin baya, lokacin da ake aurar da yarinya tun tana da ƙarancin shekaru, wato daga shekara bakwai zuwa goma, wasu iyayen da suka aurar da ‘yarsu a irin shekarun sukan haɗa ɗan kayan abinci daidai ƙarfinsu su kai ‘yar da su.
Fa’idar yin hakan a wurinsu shi ne, za su taimaka wa mijin ciyar da ita zuwa lokacin da ta isa zama mace. Wato dai za su yi tarayya wurin ciyar da ‘yar kafin ta zama mace da zai iya sakin labule da ita.
Ɗaya daga cikin dalilan da suka bambanta auren wuri da ake yi da da kuma na yanzu shi ne, kawar da kai ga yarinyar har zuwa lokacin da ta isa a kusance ta. Yana ɗaya daga cikin dalilan da ke sa auren wuri a baya ba ya tare da ƙalubale kamar na yanzu.
A inda aka fito, miji zai yi renon yarinya ne a lokacin da aka aura masa ita a ƙarancin shekaru, kuma sukan ba wa yaran damar sakewa da su sosai, wanda ko da za su kusance su yayin girma ba zai zama na ƙarfi ba kamar yadda ake yi yanzu.
Kada mu saki layin darasin namu, zancen dai shi ne, sha’anin gara ba ta da muhalli a Musulunci, saidai muhalli a mahangar magabata da suke duba ya kamata, duk da hakan ba su taɓa danganta abinda suka yi da addini ba, kuma ba su taɓa umurtar wani da ya aikata ba, domin kyautatawa ce da ake yi idan an yi sha’awar yi ko kai mai yi kana da zarafi ko kaga dacewar yin hakan.
Ya ku iyaye ku sani, wahalar aure ko tsadar aure da ke barazana ga matasanmu, da ke hana ‘ya’yanmu mata samun mazajen aure, abu ne da mu muka janyo da hannunmu, domin babu ɗaya daga cikin ababen da muke wahala da su da suka zama dole a Musulunci.
Idan mun yi a baya, don muna da halin yi, to mai zai hana mu bar su a lokacin da suke wahalar da mu? Idan muka kashe manyan al’adu da ke gurgunta yunƙurin matasanmu kan aure, tabbas za mu ga yadda al’ummarmu za ta ƙayatu, ta hanyar ƙarantar zinace-zinace da kuma rayuwar shashanci da matasa ke yi.
Da yawa a matasan da ke kwaɗaituwa da aure za su iya riƙe mace, su ciyar da ita har da buƙatunta daidai gwargwado, saidai yadda za su iya tara kuɗaɗe masu yawa da za su haɗa kayan aure zuwa sauran al’adu ne babbar barazana gare su.
Idan da za a sawwaƙa, a daina kallon komai sai auren, da an rufawa juna asiri fiye da tunaninmu. Idan matashi na da abin yi da zai iya ciyar da kansa da matar da zai kawo, ko ɗaki yake da shi a gidansu na gado ba laifi ba ne don an yi masa aure.
Ita kuma yarinya ko uwarta ba ta ajiye ko cokali ba, matuƙar ‘yar ta isa aure, kuma ta samu mai hankali, to ku yi mata aure, ababen da za a yi amfani da shi su nema daga baya, kamar yadda idan Allah Ya masa buɗi zai gina gida ko ya kama hayar gida da ya fi wanda aka kawo ta a ciki.
Mafi alheri daga aure, shi ne wanda aka sawwaƙa a cikinshi.
