
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tsige Daraktan kamfanin buga kuɗi (NSPM), Ahmed Halilu tare da wasu manyan ma’aikata guda huɗu.
Ahmed Halilu, ɗan uwa ne ga Aisha Buhari, matar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari wanda aka naɗa a watan Satumban 2022 a lokacin gwamnatin Buhari.
Sauran waɗanda aka tsige sun haɗa da; Ado Ɗanjuma, Daraktan harkokin rijistar masana’antu; Chris Orewa, Daraktan gudanarwa reshen jihar Legas; Tunji Kazeem, Daraktan kundaddakin tsaro; da Victoria Irabor, Sakatariya, wacce matar Janar Lucky Irabor ce, tsohon shugaban harkar tsaro.
Daraktan gudanarwa reshen Abuja, Abubakar Minjibir shi ne babban Darakta na wucin-gadi. Sai dai, babu wani bayani da ya nuna dalilin ɗora shi bisa kujerar.
Wani babban jami’in babban bankin Nijeriya (CBN) ya tabbatar da korar ma’aikatan da abin ya shafa.
Sannan, an yi hukuncin ne bayan da wani mai bincike na musamman Jim Obazee da shugaba Tinubu ya naɗa, ya fitar da wani rahoto kan nazari game da ayyukan CBN ƙarƙashin gwamnatin shugaba Buhari. Rahoton ya bayyana yadda NSPM ya bada gudunmawa wajen batun tsarin sauya fasiln kuɗi wanda tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya jagoranta wanda hakan ya zama sanadiyyar takura wa al’umma da sana’o’i a Nijeriya.
Kamar yadda rahoton ya nuna, lokacin da Emefiele ya samar da tsarin sauya fasiln, ya umarci Halilu ya sauya fasalin tsohon kuɗin inda ya ce yin hakan zai ɗauki tsawon lokaci kafin cika ƙa’idodin da ake buƙata.
Duk da wannan bayanin, Emefiele ya yi buris, inda ya yo hayar wani ɗan ƙasar Ingila, De La Rue kan fam 250,000 domin yin aikin a takaitaccen lokaci.
Bayan kammala aikin ne, NSPM ya buga sabon kuɗin wanda bai kai adadin da ake bukata ba, wanda sanadiyar haka ne aka shiga matsanancin rashin isassun kuɗaɗe a hannun al’umma a Nijeriya.
