
Daga UMAR NURA
Kafin mu kai ga bayyana ra’ayinmu game da sarƙaƙƙiyar yarjejeniyar Samoa, za mu so mu sanar da al’umma cewa, Ƙungiyar Concerned Northern Elite Forum ta masu kishin al’ummar Arewa, ba ta siyasa, kasuwanci ko jam’iyya ba ce.
Manufarmu ita ce bayar da kariya ga Arewa da ma Nijeriya bakiɗaya ta hanyar gwagwarmaya da kuma yaƙar duk wani mataki ko wani al’amari da zai haifar da matsala a cikin al’umma.
Kamar yadda aka sani, a ranar 28 ga Yuni, 2024 Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar Samoa a sakatariyar ƙungiyar ƙasashen Afrika, Caribbean da Pacific (OACPS) da ke Brussels, babban birnin ƙasar Belgium. An yi yarjejeniyar haɗakar ne tsakanin ƙasashen ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) a gefe guda da kuma da na OACPS a ɗaya ɓangaren.
An fara tattaunawa kan batun yarjejeniyar ne a shekara 2018, a cikin maudu’an zaman Majalisar Ɗinkin Duniya na 73. A ranar 15 ga watan Nuwamban shekarar ne duka ƙasashen EU 27 da na OACPS 47 cikin 79 suka sanya mata hannu a Apia da ke Samoa.
Yarjejeniyar tana da saɗarori 103 da suka ƙunshi abubuwan da aka yi tarayya a kan su da kuma kasafta shiyyoyin bisa yarjejeniya da aka haɗu a kai gida uku: Afirka-EU; Caribbean-EU da Pacific-EU. Kowace shiyya, za ta mayar da hankali wajen warware matsalolin waɗannan shiyyoyin.
Shiyyar ɓangaren Afirka ta ƙunshi ɓangarori guda biyu; na farko shi ne samar da tsarin haɗin kai, sai kuma na biyu wuraren haɗin kai, wanda ya ƙunshi sanyawa da kula da bunƙasa tattalin arziƙi da kuma cigaban al’umma da ƙasa; kula da muhalli, kula da albarkatun ƙasa, da kuma sauyin yanayi; zaman lafiya da tsaro; ƴancin ɗan Adam, demokraɗiyya da shugabanci; shige da fice da bulaguro.
Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar 28 ga watan Yuni, 2024. An yi haka ne bayan nazari mai zurfi da shawarari da kwamitin Ministoci ya yi a ƙarƙashin jagorancin ma’aikatar kasafi da shirin tattalin arziƙi tare da taimakon ma’aikatun harkokin waje da na shari’a.
An tabbatar cewa babu ɗaya daga cikin duka saɗarorin 103 da ta ci karo da dokar Nijeriya ta 1999 da ma wasu dokokin da su ke kafin wannan. Bugu da ƙari, a lokacin da Nijeriya ke sanya hannun, ta haɗa da wata takarda mai kwanan wata kamar haka; 26 ga watan Yuni, 2024 wacce ke ƙunshe da bayanin cewa duk wani batu da ke cikin yarjejeniyar da ya ci karo da dokokin Nijeriya, to ba za a amince da shi ba.
Akwai buƙatar al’umma su sani cewa, akwai dokar da ke ƙin amincewa da alƙara jinsi ɗaya a Nijeriya, kamar yadda aka zartar a shekarar 2014.
Mun yi zurfin bincike game da lamarin kuma mun yi magana a kai, sannan mun tattaro ra’ayoyin farfesoshi 18 a faɗin duniya waɗanda mafi yawancin su ƴan ɓangaren Shari’ar Muslunci ne.
Ya na da muhimmanci mu tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa, gwamnatin shugaba Tinubu ba ta shiga kowace irin yarjejeniya da ta zama fitina ga al’ummarta ba. A yayin tattaunawar yarjejeniyar, wakilan Nijeriya sun yi matuƙar kiyaye dokokin da aka yi musayarsu a 2018 tsakanin EU da OACPS a yayin tsarawa.
Bincikenmu ya bayyana cewa, wasu manyan ƴan adawa ne suka ɗauki nauyin bazuwar labarin daga wata Jaridar ƙasa, domin janyo suka ga gwamnatin Tinubu, a madadin bai wa ƴan Nijeriya damar samun romon dimukraɗiyya.
Bincikenmu ya qara nuna cewa, koke-koke game da ƴancin auren jinsi (LGBTQ) a yarjejeniyar ba wani abu ban ne illa aikin ƴan adawa waɗanda ke cigaba da ɗaukar nauyin faɗa da gwamnatin ta hanyar kafafen yaɗa labarai musamman a Arewacin Najeriya.
Haka nan, mun gano cewa, wasu maƙiya cigaban Arewa sun shirya zanga-zanga a jihohin shiyyar guda uku. Sobada haka, mu ke kira ga matasa kar su yarda wani ɗan adawa ya yi amfani da su da sunan zanga-zangar Samoa wanda hakan kan iya haifar da tashin hankali ga zaman lafiyar yankin.
Yanzu ba lokaci ba ne na siyasa, lokaci ne na shugabanci da cigaba, don haka abin takaici ne a ce wasu ƴan adawa sun fake da batun Samoa wajen amfani da matasa yayin haddasa fitina a Arewa.
Mu Ƙungiyar Concerned Northern Elite Forum mun haɗu a kan cewa wajibi ne a kanmu a matsayinmu na muryar jama’a, mu samar da tabbatacce, gamsashshe kuma fayyataccen bayani game da labarin ƙarya ga al’umma kamar batun Samoa da ma wasu da kuma dukkan yunƙuri na cin mutuncin gwamnati da kuma sauya tunanin mutum a kan ra’ayoyinsu game da shi.
Wannan al’amari ya yi wuri, don haka mu na gargaɗi ga al’umma da su ƙaurace wa amfani da bayanan da aka yaɗa su da gangan don cimma wata manufa ko kuma labaran ƙarya ko kuma wasu su yi amfani da su a matsayin makaman sukar ƙoƙarin shugaban ƙasa na tanadi mai kyau da yake da shi wa Arewa wajen taɓa mutuncinsa.
A bayyane yake cewa, Ƙungiyar Concerned Northern Elite Forum ta yi kira ga shugaba Tinubu da ƴan tawagarsa su cigaba da kasancewa cikin lura da kuma ƙoƙarinsu kan cigaban ƙasa. Muna kira ga shugaban ƙasa ya sani cewa akwai kamfe-kamfe na farfaganda da ke yaƙar gwamnatinsa, sannan kuma ya mayar da hankali wajen cika alƙawuran da ya yi wa ƴan Nijeriya.
Ya na da muhimmanci ga gwamnatin ta tsayu a kan burace-buracenta da fuskantar ƙalubalen da ke gabanta, sannan ta yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da an samu gobe mai cike da albarka a Nijeriya. Gwamnatin sai ta nazarci waɗannan yunƙuri tare da daƙile su domin tabbatar da ɗorawa ga cigaban ƙasa.
A matsayinmu na ƙungiya da ta sadaukar da kanta ga cigaban ƙasarmu Nijeriya, ba za mu amince wa wasu ko wani ba da za su/zai yi amfani da yarjejeniyar Samoa wajen yin ƙage ga gwamnatin ba. Wannan rashin adalci ne daga abokanan adawar siyasa da ke sukan cigaban da ake samu da kuma rashin adalci ga gidajen jarida wajen ruwaito labaran suka, da inda aka gaza da kuma aibatawa da ƙasar ke fuskanta.
Nura shi ne Shugaban Ƙungiyar Concerned Northern Elite Forum, ya rubuto daga Kano
