
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wani ɗan adaidata sahu ya kashe kansa sakamakon karɓe masa babur da wasu jami’an hukuma suka yi a ƙaramar hukumar Ikorodu dake jihar Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya auku ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli inda yayin da matuƙin ke tafiya kan wata hanya, sai ya yi artabu da jami’an kan wani laifi da ya aikata.
Da nan ne, sai jam’ian suka karɓe adaidata sahun kana suka tafi da shi zuwa ofishinsu dake rukunin gidajen Jubilee a babbar hanyar Ikorodu-Sagamu.
An samu gazawa a yunƙurinsa na zuwa karɓo babur ɗin nasa domin kuwa ya yi ƙoƙarin tada hayaniya, amma hakan bai sa ya yi nasara ba.
Daga nan ne sai ya fita wajen ginin inda akwai wata bishiya da kuma ofisoshin jami’an hukumomin kiyaye haɗurra, da na kula zirga-zirgan ababan hawa (LASMA) inda a jikin bishiyar ne ya rataye kansa kamar yadda wata ɗaukar ‘video’ ta nuna.
A lokacin da yake magana kan al’amarin, mai magana da yawun LASMA, Taofiq Adebayo ya musanta cewa akwai hannun hukumar ko jami’ansu a cikin faruwar lamarin, hasali ma ya ce babu wani adaidata sahu da ɗaya daga cikin jami’ansu ya karɓe a wannan yankin.
