An kuɓutar da limamin coci bayan sati biyu da sace shi a Zamfara

Spread the love


Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An sako Fafa Mikah Suleiman, Babban Limamin Cocin Katolika na St. Raymond da ke Damba, Gusau a Jihar Zamfara, bayan da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi tsawon makonni biyu.
An tabbatar da sakin sa ne a ranar Lahadi, 7 ga Yuli, 2024, a cikin wata sanarwa da Pascal Salifu, Daraktan Sadarwa na Diocese na Katolika a Sokoto ya fitar.
“Mun yi matuƙar farin cikin sanar da sakin Fr Mikah Suleiman, wanda aka yi garkuwa da shi ranar 22 ga watan Yuni, 2024,” inji sanarwar.
“Mu na miƙa godiyar mu ga Allah da ya kiyaye shi da kuma duk wanda ya yi addu’a da goyon baya a wannan lokaci. Muna kuma godiya ga hukuma da duk masu hannu wajen ganin an sako Fr Mikah. A halin yanzu yana samun kulawa da tallafin da ya kamata.”
Salifu ya kuma buƙaci a ci gaba da yi wa Baba Suleiman addu’a yayin da ya fara samun sauƙi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya tabbatar da yin garkuwa da mutanen a ranar Asabar.
“Eh, lamarin ya faru da sanyin safiyar yau. An yi garkuwa da limamin coci daga gidansa. Ba a sanar da mu nan take ba, amma mun tura rundunarmu ta dabara don bin diddigin masu garkuwa da mutane da nufin ceto wanda abin ya shafa ba tare da wani rauni ba.”
A baya Nuhu Iliya, Muƙaddashin Shugaban Katolika na Sokoto, ya buƙaci al’ummar Kirista da su yi addu’ar Allah Ya sa a sake shi cikin gaggawa.”
A wani labarin kuma, a farkon watan Yunin 2024, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Baba Gabriel Ukeh, shugaban cocin St. Thomas Parish da ke unguwar Zaman Dabo a ƙaramar hukumar Zango Kataf a jihar Kaduna, a farkon watan Yunin 2024. Lahadi, kamar yadda Ɓicar Janar (Pastoral) Emmanuel Kazah ya bayyana a wata sanarwar manema labarai.

By ukarofi