NNPP ta zargi Tinubu da goyon bayan Aminu Ado Bayero

Spread the love


Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Jam’iyyar NNPP mai mulki a Jihar Kano, Dr Hashimu Dungurawa ya zargi shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da hannu a hana ruwa gudu a rikicin masarautar Kano da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata game da nasarorin da jam’iyyar NNPP ta samu a cikin shekarar da ta gabata, Dungurawa ya bayyana cewa hakan hujja ce kan yadda aka turo sojojin Nijeriya, ’yan sanda, DSS, da sauran jami’an tsaro domin su bai wa Sarki Bayero kariya ta musamman, saɓanin muradun gwamnatin jihar.
Dungurawa ya yi gargaɗin cewa katsalandan ɗin da ake zargin shugaba Tinubu ya yi a kan batun masarautar Kano ka iya janyo koma baya a zaɓen 2027.
Ya ci gaba da cewa, “Matsayin ku game da ricikin Masarautar Kano tabbas zai yi tasiri a kanku a shekarar 2027 domin idan kuna tunanin za ku iya amfani da shi don samun nasara a Kano, to za ku gane kuskurenku idan lokacin ya yi.”
Ya kuma soki yadda ake amfani da alaƙar Sarki Bayero da ƙabilar Yarbawa a matsayin wata hanya ta ci gaba da riƙe muƙaminsa a Kano, ya kuma buƙaci shugaban ƙasar da ya warware rikicin masarautar Kano ta hanyar tsige Sarkin da aka tsige daga jihar.
Dungurawa ya kuma bayyana cewa jam’iyyar NNPP na shirin tsayar da Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa Kwankwaso ne zai zama shugaban ƙasar Nijeriya.
Bugu da ƙari, Dungurawa ya yi kira da a sake duba sakamakon zaɓen 2019, yana mai cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, bai yi nasara ba bisa ƙa’ida a karo na biyu a matsayin gwamna.

By ukarofi