Daga UMAR AkILU MAJERI Dutse
A wani samamen haɗin gwiwa tsakanin dakarun hisba ‘yan sandan, jami’an civil defense da na ‘yan sandan farin kaya (DSS) da suka kai kasuwar ƙauyen Tage da ke Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa a makon jiya sun sami nasarar damƙe mutane 45 da ake zargin su da fakewa da guzuma suna harbin karsana.
Kwamandan Hisba na Shiyyar Kafin Hausa, Malam Abdulƙdir Zakari Kafin Hausa, shine ya tabbatar da faruwar hakan, inda ya ce, mutanen da suka kama ɗin sun haɗa da maza da mata da mawaƙan garaya da masu rawar bori da suke fakewa da sunan sana’ar kamun kifi da yin tuwo-tuwo a kasuwar.
Ya ce, kai samamen ya biyo bayan bayanai da Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa ta samu ne akan yadda ake aikata laifuffuka marasa daɗin ji, inda haka yas a mai rikon kujerar karamar hukumar, Alhaji Muktar Muhammad Maigatari, ya bayar da umarnin akai samame kasuwar, domin hana duk wani fasadi a kasuwar.
Ya ƙara da cewa, dakarun hisbar tare da taimakon sauran abokan aiki sun cafke waɗanda ake zargin ne a wasu bukkokin kara da suka gina a gefen kasuwar, waɗanda ake zargin suke sana’ar karuwanci, maza suna shiga suna aikatan fasadi da su.
Ya ce, kamar yadda bincikensu ya nuna, mafi yawan waɗanda aka kama ɗin matasa ne ƙanana waɗanda suke da ƙarancin shekaru, ba su wuce su yi aure ba, suka tsunduma harkar karuwanci, amma suka fake da sana’ar yin tuwo-tuwo a kasuwar, yayin da sauran mazan kuma suka fake da sana’ar kamun kifi, amma ba su da wata sana’a sai rawar bori da kiɗan garaya da aikata ƙananan laifuffuka da suke neman addabar al’ummar yankin.
Ya ƙara da cewa, kashi 80 cikin 100 na waɗanda aka kama ɗin ‘yan asalin Jihar Bauchi ne da ke da iyaka da Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa.
A lokacin da suke amsa tambayoyin ‘yan sanda bayan da aka kammala tattara su a caji ofis da ke Kafin Hausa, dukkansu sun amsa laifinsu da ake tuhumar su da aikatawa na yawon banza da aikata baɗala tare da ƙoƙarin aikata miyagun laifi.
Duba da iƙirarin da sukai y da bakinsu ya sa jami’an hisba suka gurfanar da su a gaban manyan kotunan shari’a da ke ƙaramar hukumar, domin su ma su girbi abinda suka shuka, wato a kotun Upper Sharia Court da kuma Higher Sharia Court.
Yayin da suke amsa tambayoyin alƙalan kotunan biyu, dukkansu sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su. Saboda haka ne aka yanke masu hukuncin biyan tara ta kowanne mutum ɗaya zai biya tarar Naira 10,000 ko kuma ya tafi gidan yari ya yi zaman wa’adi na wata uku, domin hakan ya zama izina ga masu irin wannan hali.
Ya ƙara da cewar, mutun 10 ne kacal daga cikin su 45 da aka zarta wa hukuncin suka iya biyan tarar kuma aka sallame su nan take tare da yi masu gargaɗin kada a sake kawo su gaban wannan kotun, kuma duk wanda ya yi sakaci aka sake kawo shi, zai kwashi kashinsa a hannu.
Yayin da sauran mutane 35 da suka haɗa da maza da mata suka kasa biyan tarar su kuma, alƙalan kotunan biyu suka sa aka ingiza ƙeyarsu zuwa gidan maza, domin hakan ya zama darasi ga ‘yan baya.
Saboda haka ne ma shugaban riƙo na Kafin Hausa, Muktar Maigatari, ya ce, ƙaramar hukumar ba za ta lamunci aikata baɗala ba a faɗin yankin ƙaramar hukumar, inda ya ce, a shirye ya ke ya ɗauki matakin da ya dace wajen ladaftar da duk waɗanda suka kama ya na aikata fasadi.
Ya kuma shawarci al’ummar Tage da sauran al’ummar ƙaramar hukumar su sanya ido akan duk wata baƙuwar fuska da ba su amince da ita ba tare da mayar da ƙaramar hukumar maɓoyar duk wasu masu aikata laifi a yanki. Ya Kuma gargaɗi dukkan mutanen da suke ƙoƙarin haifar da fasadi da su gaggauta ficewa daga yankin. Idan kuma sun ƙi doka za tai y aiki akan su.
Ya ƙara da cewar, ƙaramar hukumarsa a shirye ta ke ta yi aiki da hukumar hisba da sauran jami’an tsaro wajen ganin sun taimaka mata wajen tsaftace ƙaramar hukumar da nufin yin waje da mutane marasa gaskiya daga cikin al’umma.
