Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP za ta faɗi warwas a zaɓen 2027 saboda matsayar da ta ɗauka kan rikicin masarautar Kano.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas, ya bayar da hujjar cewa lamarin zai yi mummunar tasiri ga damar zaɓen NNPP, wanda hakan zai bai wa Shugaba Bola Tinubu nasara.
Ya yi iƙirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ba shi da wani shiri na zama shugaban Nijeriya.
A cewar Abbas, jam’iyyar APC a yanzu ta samu haɗin kai da farin jini, yana mai hasashen cewa za ta samu ƙarin kasshi uku na ƙuri’u a Jihar Kano idan aka kwatanta da zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, saboda gazawar gwamnatin Kano a yanzu.
Abbas ya soki rahoton da kafafen yaɗa labarai suka yaɗa da shugaban NNPP na jihar Kano Hashimu Dungurawa, inda ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP da shugabanta na ƙasa, Kwankwaso ne za su warware rigingimun masarautar da ke faruwa.
Dungurawa ya yi ikirarin cewa batun Masarautar na iya yin illa ga yunƙurin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takara a 2027.
Abbas ya yi watsi da wannan ikirarin da cewa wata alama ce ta gazawar NNPP a matakin jihohi da ƙasa bakiɗaya.
Abbas ya yi tsokaci kan rikicin cikin gida a cikin jam’iyyar NNPP, wanda ya ce ya fallasa kurakuran ta. Ya ba da shawarar takarar shugaban ƙasa na Kwankwaso a 2023 dabara ce ta tabbatar da dacewa, sauƙaƙe burin surukinsa na siyasa, da kwato Kano daga APC.
Abbas ya bayyana cewa Kwankwaso ya samu ƙuri’u 1,454,649 (6.23% na ƙuri’u 6.23) akasari daga Kano, ya kuma yi tambaya kan yadda ɗan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi ya zarce Kwankwaso a wasu jihohin Arewa.
Shugaban Jam’iyyar APC ya jaddada cewa burin gwamnatin tarayya na rikicin masarautar Kano shi ne tabbatar da bin doka da oda domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Abbas ya tunatar da jam’iyyar NNPP irin kayen da ta sha a 2019 da kuma ‘yar tsirar da ta samu a 2023, duk da cewa tana da ɗan takarar shugaban ƙasa daga jihar Kano. Ya soki ayyuka da manufofin gwamnatin NNPP ƙarƙashin Gwamna Abba Yusuf, yana mai nuni da cewa waɗannan za su yi wa NNPP illa a zaɓe mai zuwa.
Ya yi nuni da cewa yayin da sauran gwamnonin jihohi ke cika shekara guda da gudanar da ayyuka, jam’iyyar NNPP ta tsunduma cikin batun dokar Masarautu.
Ya yi hasashen cewa mutanen da ayyukan gwamnati mai ci ke shafa ba za su goyi bayan jam’iyyar NNPP a zaɓe mai zuwa ba.
A ƙarshe Abbas ya tabbatar wa da shugaba Tinubu da shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa cewa yanzu jam’iyyar APC ta jihar Kano ta ƙara haɗe kai da kuma shirin samun ƙuri’u masu yawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
