DAGA MUKHTAR YAKUBU
Da alama dai mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala ya zama mazari ba ka gaba a fagen waƙa ta yadda duk inda ya sa gaba sai yanayin ya dace da shi. Shi mawaƙin fada ne, mawaƙin siyasa ne mawaƙin ‘yan kasuwa, baya ga kasancewar sa mawaƙin faɗakarwa.
Wani salo da mawaƙin yake da shi wanda ya bambanta shi da sauran mawaƙa shi yanayin waƙar da yake yi da kowanne salo ba ki. Kamar yadda ya yi waƙa Kukuma, ya yi waƙa da tafi ya yi waƙa da Bandiri. Kuma a ‘yan kwanakinnan aka ji shi ya fitar da wata sabuwar waƙar sa da Kuntiki.
Wakilinmu ya tattauna da Aminu Ladan Abubakar Ala don jin yadda alaƙar sa ta kasance da kiɗan kuntiki, kukuma da sauran kayan kaɗe-kaɗe da yake yin amfani da su.
In da ya fara da cewa. ” To ni marubucin waƙoƙi ne wanda nake rubutu waƙoƙi a rubuce sannan kuma sai na karanta. Kuma wannan wani tsari ne da masana suka tabbatar mana da cewa mu makaɗan baka ne ko marubuta waƙoƙin baka. Sannan kuma wasu manazarta sun hukunta mu a kan marubuta waƙoƙi na zamani, saboda haka sai ake kallon mu a matsayin makaɗan baka ko mawaƙin baka na zamani.
To inda muka fada da daman aiki ne na manazarta. Wanda ni kuma abin da nake so mutane su gane, tsawon lokaci ni na fara waƙoƙin nan ma a daɓe ne, kamar misali idan aka yi duba zuwa 2007 a lokacin Malam Ibrahim Shekarau yana Gwamnan Jihar Kano, an ƙaddamar da wani shiri na Adaidaita Sahu da aka ƙaddamar da shi a ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano. To a lokacin muna bin Sarkin Kano muna yin waƙar, amma babu kiɗa tafi. Misali irin waƙar ‘Rayuwa a Duniya Tana Ban Tsoro’ da makamantan su, irin su ‘Sababin Mutuwar Aure’, su nake yi a lokacin da wasu waƙoƙi na yabo, duk a ƙarƙashin Hukumar Adaidaita Sahu.
To ka ga muna yin waƙar ma haka da ka sai dai mu haddace mu karanto baitukan. Wannan ya sa ni nake ɗaukar kiɗa a waƙa a matsayin wani abu da zai ja hankali , ko an yi shi da gwangwani, ko kwalba, Kukuma Lalajo, Amada Kuntigi, saboda haka duk abu ɗaya ne. Abin da zai jawo hankali ne, saboda haka idan na tsara waƙar da na ga za ta yi tsari da kukuma da ita zan yi. Kamar misali shawarar da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya ba mu, ya ce za a yi taron tunawa da Ɗan Maraya Jos, me zai hana mu ɗauki wata waƙarsa mu yi haɗaka don mu yi masa ta’aziyya. Wannan ce ta sa muka shirya waƙar ‘Mai Akwai da Babu’ waƙar Ɗan Maraya ce muka yi haɗaka ni da Fati Nijar.
Ka ga waƙar ta kuntiki ce, amma saboda Ɗan Garba Sufa yana tare da mu a lokacin sai muka buga mata kukuma muka haɗa da kayan kiɗa na zamani, kuma ta zo ta yi fice, duk da asalin waƙar ta mai kuntiki ce kuma da kuntiki aka yi ta.”
Dangane da sabuwar waƙarsa da ya yi kuwa da kukuma cewa ya yi,
“To shi abin da ya faru Babangida Kaka Dawa shi ne ya kawo mini ziyara, a lokacin har ma nake cewa za a yi bikin ‘ya’yana . Ya ce zai yi mini waƙar talla don a tallata bikin, a nan ya yi ta. Sai kuma na ce da shi to, ni ma sai ka ɗan yi mini wasu kiɗoɗi haka da zan yi amfani da su na yi wasu waƙoƙi na daban. To wannan ya sa aka ji ni da waƙar kukuma har na yi wa Aminu Ado Bayero waƙa. Saboda haka muna yi muna saka kalangu, da sauran kayan kaɗe-kaɗe, amma dai ba mu cika bai wa kiɗa muhimmanci ba. Saboda ba da kayan kaɗe-kaɗe muka taso ba a tsarin rubuce-rubucen waƙoƙin mu. Asalin ma ni ina kallon su Mudi Spiking ne su Mu’azu Hadeja. Don ka ga waƙoƙinsu da aka yi su a kan ma’auni na Baharin Wawa, to amma ina iya ɗaukar su na ɗora su a kan kiɗa na zamani kuma su tafi a hakan.
Misali kamar waƙar Muhammad Uba Adamu, akwai waƙoƙinsa waɗanda ba juya su na yi ba. Yadda suke haka na ɗauke su, sai dai na gabatar da su cewa, wannan waƙar ba tawa ba ce ta Muhammad Uba Adamu ce, ni biyawa na yi na kaisu ‘studio’ aka ɗora musu kiɗa wajen waƙoƙi huɗu na ɗauka.
Sai kuma waƙar Mudi Spiking da na ɗauka wadda ita haka na karanta ta gayanta a situdiyo. A yanzu ma akwai waƙoƙin Sa’idu Zungur da nake so na ɗauka na karanta na ɗora musu kiɗa, kamar dai yadda na yi wa waƙoƙin Abubakar Ladan wanda su ma haka yake yin su babu kiɗa ba komai. Amma sai na ɗauki waƙar ‘Haɗa kan Afirka’ ba tare da na ƙara ko na canza wasu baituka ba. Haka yadda yake yi ni ma na bi na rera.
Saboda haka mu shiga Studio mu taba wini abu na kiɗa ko jita fuman girke ko jarka ce za mu buga ta bayar da ma’ana duka mu abin da muka cauki kiɗa kawai ƙararrawa da zai jawo hankali don mu isar da saƙon da muke so mu isar. Shi ya sa duk wani kiɗa da zai ja hankali ya yi mana daɗi, musamman kaɗe-kaɗe na gargajiya da muke so mu dawo da su, don a san muna da irin sauti namu na Hausawa kada ya ɓace. To wannan yana daga cikin abin da ya sa nake dakko su nake yin amfani da su, da ma kara-karan harshe wanda daga mutum ya ji ya san ba wani Balarabe ko wani Ba’indiye ne zai yi waƙar, don haka muka fi bada ƙarfi a kan al’adar, don haka ni zan ci gaba da yin haka domin inganta rayuwarmu ta gargajiyar Hausawa yadda za farfaɗo da al’adar,” Inji mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala.
