
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ministar al’adu, Barista Hannatu Musa Musawa ta shiga sahun al’umma da dama wajen taya ɗaya daga cikin jigo a fagen ilimi, Farfesa Wole Soyinka murnar cikarsa shekaru 90 a duniya.
Wata sanarwa da mai bata shawara kan harkokin yaɗa labarai, Nneka Ikem Anibeze ta fitar, ta ce ministar ta taya Farfesan murnar cimma nasarar kai wa matakin nasara irin haka gami da jinjina masa bisa ga halin juriya da ya siffanta da shi.
Musawa ta kuma yi farin cikin sauya sunan cibiyar al’adu ta ƙasa zuwa cibiyar al’adu ta Wole Soyinka wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi inda ta ce ta ji daɗin hakan da aka yi.
Kazalika, ana cigaba da sabonta ginin cibiyar wanda aka fara tun shekaru uku da suka gabata da taimakon kwamitin ƴan banki na babban bankin Nijeriya wanda shugaba Tinubu ya shirya sake bikin buɗe ta a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 da ya yi daidai da cikar ƙasa shekaru 64 da samun ƴancin kai.
