Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin wasu hukumomi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da naɗa Baffa Ɗan Agundi a matsayin sabon Darakta Janar na cibiyar bunƙasa ƙwazon aiki ta ƙasa (NPC).

Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya ce, Ɗan Agundi shi ne tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokokin jihar Kano kuma tsohon rijistira a babban kotun Shari’a na jihar.

Tinubu ya kuma naɗa tsohon mataimakin gwamnan jihar Nassarawa, Silas Agara a matsayin Darakta Janar na cibiyar samar da ayyuka (NDE). Agara, ɗan kasuwa ne kuma jigo a harkar wasanni.

Haka kuma, “a hukumar kula da albarkatun ruwa NIHSA, Tinubu ya naɗa Umar Mohammed a matsayin sabon Darakta Janar” inji Ajuri.

Umar Mohammed, masinin zanen gine-gine ne kuma masanin fasahar gini da kuma ilimin muhalli. Tinubu ya naɗa shi ne domin inganta harkokin samar da ruwa a faɗin Nijeriya musamman ta hanyoyin fasahar zamani.

A Wani ɓangaren kuma, shugaba Tinubu ya naɗa tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Bashir Lado Muhammad a matsayin mai bashi shawara kan lamuran Majalisar Dattijai.

Lado gogaggen ɗan siyasa ne, ɗan kasuwa kuma tsohon Darakta Janar na hukumar hana safarar ɗan adam (NAPTIP).

Kazalika, a cibiyar kula da harkokin kiyaye dokokin ƙasa, Tinubu ya naɗa Dakta Mainasara Umar Kogo a matsayin shugaba. Dakta Kogo ƙwararren lauya ne kuma mai sharhi a kan lamuran Shari’a, tsaro, tattali, siyasa da kuma harkokin ƙasa-da-ƙasa.

By Babaji