Alamu sun nuna cewa, wakilan Jaridar Blueprint da The Nation Abduraheem Aodu and Abdulgafar Alabelewe sun sami ƙuɓuta daga hannun wanda suka yi garkuwa dasu.
Wannan ya fito ne daga bakin shugabar ƙungiyar yan jaridu na ƙasa reshen Jihar Kaduna, Asma’u Yawo Halilu.
Ta bayyana wannan saƙon ne ta manhajar WhatsApp inda ta ce” ƙungiyar na miƙa sakon jinjina ga rundunar ƴan sanda reshen jihar kaduna da kuma sauran jama’a wanda suka taya mu addu’a wannan lokacin”
Jaridar Blueprint ta gano cewa ƴan jaridun suna hanyar zuwa Abuja.
