Hukumar FBI ta tabbatar da yunƙurin kashe tsohon Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump a yayin yaƙin neman zaɓe a Butler, Pennsylvania.
Wanda yayi yunƙurin yanzu haka ya mutu da wani mutum guda ɗaya. Sai kuma wasu jami’an tsaro da sun jikkata sosai, suna asibiti suna amsar kulawa.
FBI ta fitar da sanarwa cewa ” mun tabbatar da yunƙurin kashe tsohon shugan ƙasa Donald Trump a Pennsylvania.”
Sai dai hukumar baga bayyana sunan wanda ke da alhakin kai wannan mummunan harin ba.
