
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugabannin ƙasashe da dama sun nuna damuwarsu kan ji wa tsohon shugaban ƙasa Amurka, Donald Trump ciwo a wani harin kisan kai da aka kai masa a lokacin yawon yaƙin neman zaɓe.
Shugabanni da Firaministoci sun yi tsokaci kan tare da sukan tashin-tashinar siyasa gami da nuna goyon bayansu ga waɗanda ibtila’in ya afka musu a ranar Asabar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum ɗaya da kuma raunata wasu biyu a taron.
Shugabar hukumar Turai, Ursula Von der Leyen ta ce ta yi matuƙar girgiza da harin inda ta ce babu gurbin tashin-tashinar siyasa a demokraɗiyya.
Kansilan ƙasar Jamus, Olaf Scholz ya yi alla-wadai da harin inda ya ce hakan barazana ce ga demokraɗiyya.
A wani saƙon kuma, shugaba Emmanuel Macron na ƙasar Faransa ya ce harin kisan kan abin tausayi ne ga demokraɗiyyarsu inda ya jajentawa al’ummar ƙasar.
Sauran ƙasashen da suka jajentawa lamarin sun haɗa da Rasha, Ukraniya, Chana, Argentina, Bolivia, Brazil, Colombia, Chile, Misira da sauran su.
Kazalika, sun yi fatan a kammala yawon yaƙin neman zaɓen ƙasar cikin kwanciyar hankali da lumana.
