
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Tsohon shugaban Amurka kuma ɗan takarar kujerar shugabancin ƙasar a zaɓen 2024, Donald Trump ya zaɓi Sanata JD Vance, R-Ohio a matsayin wanda zai zame masa mataimaki wanda ake fatan ya zama magajinsa na siyasa yayinda ake cigaba da shirye-shiryen zaɓe.
A watan Agusta ne Vance zai cika shekaru 40 da haihuwa wanda ya kasance mai salo irin na Trump mai shekaru 78 da shugaba Joe Biden mai shekaru 81.
Trump ya zaɓi matashin ne kwanaki biyu bayan da ya tsallake rijiya da baya inda aka kai masa harbi a yayin wani yawon neman zaɓe.
Matuƙar Trump ya yi nasara, Vance shi ne zai zama matashin mataimakin shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru na uku da aka taɓa yi a tarihin ƙasar, tun bayan John Breckenridge mai shekaru 36 a shekarar 1857 da kuma Richard Nixon mai shekaru 40 da kwana 11 a shekarar 1953.
