Gwamnatin tarayya ta ba wa gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 da kuma babban birnin tarayya tallafin tirela 20 na shinkafa domin ci gaba da rabawa ‘yan Najeriya.
Da yake jawabi ga manema labarai Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, ya ce shinkafar na ‘yan Najeriya ne masu rauni.
Ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta himmatu wajen ganin ‘yan Najeriya sun samu abinci.
‘Yan Najeriya dai na ƙorafin halin ƙunci da hauhawar farashin kayayyaki.
