MAKAMASHI: Rugurguza haramtattun matatun man fetur ne mafita?

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

An daɗe, shekara da shekaru, ana ruwa kuma ƙasa na shanyewa, kuma wannan abu bai sauya ba, kuma al’amura na tafiya kamar yadda aka saba. Tun lokacin da mutanan yankin Delta, suka fahimta cewa man fetur dukiya ce kamar ɗanyen gaul ga mutumin Zamfara da Sokoto da Kebbi da Naija da Taraba da Adamawa da Borno da kuma jihar Katsina tsugunu kuwa ba za ta ƙare ba.

Ita ƙarya fure ta ke yi, ba ta ’ya’ya haka ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi, wannan ya sa ga mahakunta da sauran ‘yan ƙasa su yarda cewa rugurguza haramtattun matattun man fetur a jihohin Bayelsa da Delta da Ribas har ma a Kuros Ribas ba zai haifar da ɗa mai ido ba, illa kashe-kashen rayuka da asarar dukiyoyi na miliyoyin nairori. Wannan ɗabi’ar ɗan Adam ce a wannan sarari na Suhuhana Allah Maɗaukaki.

Dangane da haka wasu daga cikin al’umma masu ilimin zamantakewa da falsafar rayuwa su ka zo da tunani-tunani, masu tarin yawa wajen rabon dukiyar ƙasa, wato dukiyar da aka samu ba mai ita ta fuskar saye da musaya ko kuma ta hanyar gado. Wannan dukiya ta zama dukiyar ƙasa, wato mutane da dokar ƙasa ta zayyana su a matsayin ’yan ƙasa.

Kowacce ƙasa da tsarinta yaya ɗan ƙasa zai amfana daga dukiyar ƙasa. Ƙasa ire-iren ‘yan Najeriya da su ke bin tafarkin jari hujja da sunan dimukraɗiyya a na sayar da dukiyar ƙasa ga ɗaiɗaikun jama’ar ƙasa da baƙi masu zuba jari cikin dukiyar ƙasa. Su kuma ‘yan ƙasa a riƙa fincina musa ta kakkafa makaran ilii da sha’anin kiwon lafiya da tsaron rayuka da dukiyar al’umma dadai sauran fannonin rayuwa.

Duk wani ma’adani tun daga zinare da azurfa tama da baƙin ƙarfe har izuwa lu’u-lu’u da murjani da makashi shi kansa kwal da man fetur da gas da kuma “uranium”, makamshin da ake yin makamin ƙare dangi da shi bayan wutar lantarki dashi. A tsari irin na Damakaraɗiyar yammacin Turai da ƙasar Amurka gwamnati ba ta kasuwanci kai tsaye da dukiyar ƙasa, domin a wajansu gwamnati ba ‘yar kasuwa ba ce, aikin ta shi ne mulkin jama’a saboda kare rayukansu daga halaka.

Duk dukiyar ƙasa, ‘yan ƙasa da abokanan su ‘yan kasuwa a duk inda suke a duniya su ke haɗa ƙarfi da ƙarfe su sarrafa wannan dukiya ta ƙasa domin amfanin kansu, amma su na biyan haraji mai tsoka ga gwamnati, ita kuma gwamnati sai ta samar da abubuwan more rayuwa daga wannan ma’aikatan gwamnati. Saboda kowanne haraji ya na tafiya kai tsaye.

Misali, wannan haraji ana tara shi ne saboda ilimi don haka yana tafiya ne gurin ilimi, ba za tare da yi ma sa kanda garki ba, baya ga haka sai a sa ma sa masu sai do wajen kashe shi, shi a zamani ake kira “accountability” ɗari da kwabo sai ansan ina ya tafi, idan yayi ɓatan dabo za’a hukunta waɗanda aka bawa alhakin kula da wannan asusun. Ba kamar yadda kafanin NNPCL ya ke yi, shi ya ke kiɗansa, kuma shi ya ke rawarsa.

Wannan ta basu dama su ɓarje gumin su, a lalasariya sakaliya su da ‘yan barandan su, ba zaka san garwa ko nace ganga, wato salka nawa suka tono, nawa suka fita dashi zuwa kasuwar duniya, kuma kuɗaɗe nawa suka shiga Asusun gwamnati? Amsa tartibiya a yanzu ita ce, “kura da shan duka, amma gardi da karɓar kuɗi” talakan ƙasa mai dukiya, shi ɗan kallo ne da dukiyarsa.

Duk wannan bayanin namu, muna so ne musanar ta yin tsokaci, rugurguza matatun man fetur da ake yi ba daidai ba ne, ya saɓa hankali kuma ya saɓa ‘yan cin da ƙasa kan dukiyar ƙasa, baya ga haka ya yi wa ilimi takunkumi da turke da tarnaki haka kuma ya yi ma sa ɗaurin talala. Bayan kuma ilimi “katta rabu” ne, kamar yadda Muhammad Bello yake faɗa a lokacin yana karagar mulkin Sarkin Musulmai a Sokoto.

Haramun ne a yi wa ilimi shinge ko mu ce Katanga domin kuwa a tafe ya ke kamar ruwan Kogi, domin kuwa yana kwarara ne danga ne da kwanciyar ƙasa, yana tafiya yana kaucewa tuddai ya na bin kwari, saboda haka duk wata matsala shi ruwa baya haƙuri da ita sai ya mayar da martani, idan aka toshe masa hanya to sai yay i ambaliya yayi wa kansa hanya ta ƙarfi, haka ya sa yake samar da fadama, tafki ko kuma ya fita zuwa teku ta mashigi ko kuma ta tsarin “Delta” kamar yadda muke gani a kudancin ƙasan nan.

A daina kashe masu waɗannan matata, a bincika man da suke tacewa ta yaya ake amfani dashi a sauran, na’urori da suke buƙatar man fetur? Man fetur ɗin nasu yana da illah da waɗannan na’urori, wato motoci da Babura da kuma ijnina da suke bamu wutar lantarki. Idan har ba su da illah me ya sa ba za a shiga yarjejeniya da su ba kamar yadda aka yi da matatar man fetur da kamfanin Dangote nan gaba kuma za a yi da BUA.

Mu na ganin kamfanin da suke samar da bakin mai (engine oil) launi daban-daban, kuma ba’a ma’aikatar – “refinery”, ta Kaduna, ko ta Warri ko kuma ta Port Harcourt (Fatakwalba) baa shagunansu su ka harhaɗa sub a? Mene ne matsalar, idan har da matsala da za ta cutar da ‘yan ƙasa, sai a wayar musu da kai a basu dama su ci albarkacin dukiyar ƙasar su ba wai sai wasu ‘yan lele daga Amurka ko Faransa ko kuma daga Birtaniya ba.

Idan har matar karkara zata sarrafa gyaɗa ko riɗi ko ƙwallan darbejiya (dogon yaro) ko kuma zogale kuma ɗan adam ya ci, kuma ya kwana lafiya, haka kamfanoni manya-manya masu injina na tashin hankali da suka zo daga Turkiya ko Malesiya ko kuma su yi ma na waɗannan maya-mayai mu ci mu na lasar baki, abu ɗaya ne. Banbanci shi ne wannan ‘technology’, ya na jariri, wannan ‘refinery’ ta zama kamar ta Dangote, wacce tabbas tafi ƙarfin ta gwamnatin taraiya da suke Kaduna ko Warri har ma ta Fatakwal din.

Mu cire hassada da kushe da kuma ƙyashi idan har an tabbatar suna samar da makamashi da duniya za ta amfana kamar yadda ilimi ya yarda shi. Matsalar idan za’a rugurguza sama da matata 179 a bana wannan babbar matsalace, idan man fetur da suke tacewa da gaske ne, na tabbata za su rage ƙarancin man fetur din a kasuwa. Idan kunne ya ji jiki ya tsira, inji masu iya magana.

By ukarofi