Babban kotun Tarayya da ke Abuja, ta bada umarnin kamo likitan gidan yari da ke Kuje, Dr Abraham Ehizojie.
Wannan umarnin ya biyo bayan gazawar likitan wajen bayyana bayanin lafiyar babban jami’in Binance wanda yake a tsare a gidan yarin.
Idan bamu manta ba, gwamnatin Nijeriya ta kamo manyan jami’an Binance ne, bisa zargin ɓoye bayanan hada hadar kuɗi da ke gudana a manhajar su.
Mai sharia Nwite, bayan sauraren duka ɓangarorin biyu, ya furta cewa abun bai yi masa daɗi ba ganin yadda hukumomin gwamnati ba su ɗauki maganar shi da muhimmanci ba.
Don haka, ya bada umarnin a kamo mashi likitan gidan yari, sannan kuma a kao Gambaryan asibitin Nizamiye domin duba lafiyarsa.
Sannan ya ɗage shari’ar har sai 11 ga watan Oktoba domin cigaba da sauraren shari’ar.
