“Ƙanƙantata ya sa ake min kallon ƙaramar yarinya”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Masu hikimar magana na cewa, ‘Raina kama ka ga gayya’. Sau da dama mutane kan raina yadda suka ga mutum a farkon haɗuwarsu, saboda yanayin shigarsa ko halittarsa. Irin haka ne ake yi wa marubuciya Nafisa Auwal Ƙaura Goje daga Jihar Kano, kallon ƴar ƙaramar yarinya ko kuma ba ta kai a ce tana rubutu ba. Amma kuma abin da mutane da dama ba su sani ba, har a cikin marubuta, shi ne Nafisa ba ƙaramar yarinya ce, kamar yadda wasu ke tunani ba, saboda ƙanƙantar jikinta, domin kuwa yanzu haka ta kai shekaru 26 kuma tana da littattafai sun kai 12, da finafinan Hausa da ta rubuta da dama. A ƙarshen makon da ya gabata Nafisa ta karɓi shaidar zama gwarzuwa ta ɗaya a Gasar Gajerun Labarai wanda zauren Marubuta na manhajar WhatsApp ya shirya. Kuma kamar yadda ta saba gani, ana ganin ta fita karɓar shaidar samun nasarar ta a babban taron da aka gudanar a ɗakin taro na Murtala Mohammed na gwamnatin Jihar Kano, jama’a sun ruɗe da ganin wacce ta fito, kasancewar ba ta cikin fitattun marubuta da aka sani. Kamar yadda Nafisa ta shaidawa wakilin Blueprint Manhaja, ABBA ABUBAKAR YAKUBU, ta ce ita ma nasarar da ta samu ta shammaceta.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki. Mene ne cikakken sunanki da abubuwan da ki ke yi na rayuwa?
NAFISA KAURA GOJE: Sunana Nafisa Auwal Abubakar. Ni marubuciyar littattafan adabi da finafinan Hausa ce. Ina rubuta gajerun labarai, da labaran barkwanci na ban dariya, wato comedy. Ni ɗaliba ce, matashiya, marar aure.
Gaya mana tarihin rayuwarki, da inda ki ka yi karatu.
Ni ‘yar asalin Jihar Kano ce daga Ƙramar Hukumar Nasarawa, a Unguwar Birged Gama, yankin Ƙaura Goje. Na fara karatuna a makarantar firamare ta Kaura Goje, sannan na yi karatun Sakandire a makarantar sakandiren ‘yammata ta Larabci G.G.A.S.S Gama Tudu. Sai dai daga nan ban samu na cigaba da karatun boko ba, amma ina da burin hakan nan gaba. A ɓangaren karatun addini kuwa na yi makarantar Islamiyya ta Minahajil Islamiyya, waccea tun da na taso na ganni cikinta tare da sauran ‘yan’uwana, har sai bayan da na girma ne na koma wata Islamiyya ta Nana Asma’u Bint Fodio waccea a cikinta na sauke Alƙur’ani Mai Girma a shekarar 2016. Bayan na kammala karatuna na sakandire na cigaba da neman ilimi a ɓangaren, inda na karanci wasu littattafan addini irinsu Hadisai da Fiƙhu, kasancewar a wannan ɓangaren makarantar ta fi ƙarfi, kuma har zuwa yau, ina zuwa makarantar Islamiyya.
Wanne buri ne ki ka taso da shi a ranki lokacin tasowarki, shi ne har yanzu a ranki ko kin canza?
Gaskiya a rayuwata ban fara samun wani ƙawazuci ko tunane-tunane da burika na rayuwa ba, saboda ƙarancin shekaruna. Kasancewar rayuwar ƙuruciya irin ta da da yanzu, akwai bambanci. Saboda yanzu za ka samu ƙaramin yaro mai shekara goma ko takwas da manyan matsaloli sun dabaibayi rayuwarsa har yana tunani irin na manya ko hasashe fiye da lissafin shekarunsa ko burika masu tarin yawa. Sai da na fara harkar rubutu ne nasan wani abu wai shi buri, daga lokacin ne na fara samun burika a raina. Ina jin ina da burika masu yawa. Kasancewa ta mace budurwa ina da burin auren miji nagari, sannan ina da burin cigaba da karatu idan Allah ya nufa.
Tun yaushe ki ka fara rubutun adabi, kuma me ya baki sha’awa a rubutun labaran hikaya?
Na fara rubutu tun ina ƙaramar yarinya sosai, lokacin ina karatu a matakin firamare, sakamakon yawan ganin yayata da ƙawayenta suna karanta littattafan Hausa. Hakan ne ya kan ɗauki hankalina, duk da ban san me suke karantawa ba. Saboda haka, yayin da na fara koyon karatun Hausa na fara ne da littattafan Hausa na marubuta hikaya saɓanin wasu da kan koya a littattafai irin su ‘Ka Koyi Karatu’ Na Baba da Inna, ko Koyon Karatu’ na Bello Giɗaɗo. Amma ni na fara ne a wani tsohon littafi da na tsinta mai suna ‘Me Ya Fi Kuɗi?’ na Nazir Adam Salihi. Ina jin tun da na fara karantawa bana fahimta, har sai da na goge a cikinsa, daga nan ne na cigaba da karanta littattafai na yaƙi da irin labaran marubuta maza irin su Bala Anas Babinlata, Nazir Adam Salihi, Ibrahim Birniwa, da sauransu. Sai kuma littattafan yaƙe-yaƙe irin na su Marigayi Yaron Malam, da Abdul’aziz Sani Madakin Gini, daga nan na fara sha’awar rubuta nawa.
Na fara rubuta nawa labarin ne ta hanyar rubutun haɗaka da muka rubuta ni da wata ƙawata Aina’u Musa, labarin da muka sa wa suna ‘Alkyabbar Sihiri’, wanda shi ma labari ne na yaƙi. Bayan na shiga makarantar sakandire ne na sake gogewa da karatu yayin da na fara rubuta labaran soyayya da faɗakarwa. A wannan lokacin ne kuma na fara rubutun da kyakkyawan sa rai akan fitar da labarai na zuwa ga al’umma, saɓanin lokacin ina firamare.
Wanne labari ki ka fara rubutawa, kuma wa ya fara koya miki yadda ake rubutun labari?
Littafin da na fara rubutawa da sa ran zai isa ga al’umma, sannan na fara shi har na kammala, shi ne, ‘Ruɗani’. Sai dai babu wanda ya koya min rubutu, ni da kaina na rubuta, kuma babu wanda ya duba min. Sai bayan da na sayar da shi ga wani kamfanin buga littafi mai suna, Salama Bookshop, a lokacin ne mai shagon ya bani shawarwari akan yadda zan ƙara inganta rubutuna. Amma zan iya cewa, yawan karance-karance ne ya sa na goge da ganin yadda ake yi, kasancewar a lokacin na karanta labarai sun fi ɗari biyar.
Ki kan yi dogayen rubutu na littafi ne ko gajerun labarai ki ke yi?
Gaskiya ni tun farko da dogayen labarai na fara, sai bayan da na shiga ƙungiyoyin marubuta ne na koyi yadda ake rubutun gajerun labarai.
Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa? Kawo sunayensu.
Na rubuta littattafai sun kai goma sha daya. A ciki akwai ‘Ruɗani’, ‘Da Wa Na Dace’, ‘Babban Gida’, ‘So Kenan’, ‘Afrah’, ‘Labarin Aisha’, ‘Mugunta Ko Nagarta’, ‘Aminiyata’, ‘Aziza”, ‘Labarin Sa’adatu’, sai kuma littafin da na kammala kwanan nan, mai suna ‘Tauraruwa’, kuma in sha Allahu ina sa ran zan buga shi. Sannan har wa yau na rubuta gajerun labarai da dama, akwai kuma irin labaran da nake farawa na aje saboda wani dalili.
Za ki iya mana bitar saƙonnin da ke ƙunshe cikin wasu fitattun littattafanki uku?
Da farko akwai littafin Aziza, wanda na rubuta akan wata mace ‘yar kasuwa da ta mallaki dukiya mai yawa, ta yi shuhura cikin al’ummar da take rayuwa da su. Babu abinda ta rasa na farinciki sai dai duk wanda ya zo mata da maganar aure ba ta amincewa, kasancewar tana faɗa cewa akwai wanda take jira za ta aura, wanda kuma ya kasance ɗan’uwanta ne. Iyayensa su ne suka dauko ta daga gidan marayu suka mayar da ita ƴargata sai bayan tasowar ta ne ta kasance mara jin magana. Sanadinta ne ta jawo aka kashe mutumin da ya riƙe ta tamkar ‘yar cikinsa, ita ma matarsa ta rasu sanadin ganin gawar mijin nata, a lokacin ɗan su ya tafi ƙasar waje karatu, kuma tun daga wannan lokacin bata sake jin labarin shi ba. Ita ce ta cigaba da juya dukiyar mutumin har ta haɓaka ta zama attajira, kullum tana jiran dawowar wannan ɗan’uwan nata, don su zame wa juna dangi, kasancewar su ma ba ta san dangin su ba. Wata safiya ta zo ofis ɗin ta sai ta tarar da gawarshi a kwance a kofar ofishin cikin ƙasƙanci, yayin da ma’aikata suka shaida mata tsawon wata guda yana zuwa yana neman ganinta ba a bashi dama ba.
Sai kuma labarin ‘Aminiyata’ wanda na rubuta akan wata budurwa da ta haɗu da wata aljana a makarantar kwana, take bibiyarta a cikin mafarki, duk lokacin da ta kwanta za ta yi mafarkinta, bayan an yi mata aure aljanar ta dinga taya ta kishin mutumin da ta aura. Aljanar sai ta zo ta kashe ta a siffar budurwar mijin, kuma duk lokacin da za ta yi kisan sai ya kasance a gaban wani za ta yi, amma jarumar ita ma a ɓangarenta lokacin zai kasance tana tare da mijinta ko wani ɗan uwanta, wanda bayan an yi kisan idan an je kotu shaidar jarumar akan ba ita ta yi kisan ba. Za ta yi rinjaye akan zargin kisan da ake yi mata, daga ƙarshe shari’ar za ta shirirance har kuma aljanar ta kashe mutane da yawa.
Littafin ‘Tauraruwa’ yana ƙunshe ne da labarin wata budurwa mai suna Zaitun, wacce ke da ƙishirwar ɗaukaka, da neman suna. Kullum burinta ta yi suna duniya ta santa. Labarin ta ya zamo maudu’in tattaunawa a rediyoyi da jaridu.
Yayin da ɗaukaka ta zo mata, kamar yadda ta jima tana roƙon Allah a kai, sai ta zo mata ta wata mummunar sila. Lamarin ya faru ne sakamakon labarin wani ɗan ta’adda da aka sanar cewa ya mutu, ta ɗauka ta shahara fiye da yadda ma ta yi fata, amma ta zo ta yi nadama daga baya, bisa mummunan yanayin da ta faɗa ita da danginta da ƙasa bakiɗaya.
Shin kin taɓa samun wani ƙalubale a gida ko wajen sauran marubuta, yayin da kika fara rubutu, saboda ƙanƙantarki ko shekarunki?
Dukkan wani ƙalubale da na fuskanta na rashin fitar da littafi da rashin ƙarfafa gwiwa na same shi ne sanadin ƙarancin shekaruna da ake gani a gida da wajen ‘yan kasuwar littafi, wanda hakan ya kawo tsaikon fitar da littattafaina duk da na siyar musu da labarai har guda huɗu, kafin kasuwar littafi ta mutu. Mutanen gidanmu basu taɓa ɗaukar rubutun da nake yi a matsayin wani abu mai muhimmanci ba, har sai da na yi rubutun na gaji na dawo ɓangaren rubutun fim. Shi ma dai duk wanda na tuntuɓa cikin masu shirya finafinan Hausa, sai a yi min kallon hadarin kaza a watsar da lamarin sai bayan na zubar na daina na cire rubutu daga shafin rayuwata kwatsam watarana rubutun ya dawo cikin rayuwata ta fuskar rubutun barkwanci.
Abin da ya faru kuwa shi ne, wani abokin ƙanina ne ya zo yana so na rubuta masa wani labari na barkwanci, bayan na yi masa ya yi aikin, sai ya riƙa haɗa ni da masu shirya finafinai, tun abin ba ya tabbata har dai na ya fara tabbatuwa, inda na rubuta wa wani mai shirya finafinai Adamsy Boy, wani fim ɗin ‘Ɗan Waye?’ Har ma kuma fim ɗin ya fita a matsayin shiri mai dogon zango har ma an yi zango ɗaya a ciki. A dalilin silar shi ne na haɗu da marubuci Lawan Muhammad PRP shi kuma ya ja ni cikin marubuta har zuwa wannan matakin da nake kai.
Kin rubuta finafinai ya kai nawa kenan kawo yanzu?
Na rubuta finafinai da yawa, don gaskiya har ma na manta wasu daga cikinsu, amma nasan akwai ‘Ɗan Waye?’, ‘Tazara’, ‘So Bafatake’, ‘Sarƙaƙiya’, ‘Daren Farko’, ‘Makauniyar Zuciya’, ‘Ciwon ‘Ya Mace’, akwai kuma wanda a kusa kusan nan muka yi haɗakar rubutawa ni da Kabir Yusuf Anka da Jibrin Rano, mai suna ‘Ƙawaye’.
Sau nawa ki ka taɓa shiga wata gasar marubuta, da wanne labari, kuma a wacce shekara?
Na fara da shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa a shekarar 2021, amma ban san yadda gasar ta kasance ba kasancewar ba na cikin ƙungiyoyin marubuta ko ɗaya a lokacin, kuma ba na tare da kowanne marubuci. Sanarwar gasar ma na tsinceta ne a facebook, na rubuta na tura, daga nan kuma ban sake jin yadda ta kasance ba saboda bani da hanyar ji. Bayan na shigo cikin marubuta ne kuma na fara da shiga wannan gasar ta Marubuta WhatsApp Group. Zuwa yanzu kuma akwai gasanni da yawa da na shiga kamar ta ɗangiwa 2024 na shiga da labarina mai taken ‘Matar Manya’, sai ta Dutsinma shi ma a wannan shekara ta 2024, na shiga labarina mai taken ‘Babbar Matsala. In sha Allahu ina sa ran shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa ta bana, da kuma gasar Hukumar Tace Finafinai Da ɗab’i ta Jihar Kano da ita ma nake ƙoƙarin shiga duk a wannan shekarar.
Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne abin cigaba ta taɓa yi miki, don inganta rubutunki?
Ina ƙarƙashin ƙungiyar Hausa Authors Forum. A wannan kungiya na buɗi ido, a cikinta ne kuma na samu gogewar da ni kaina na yarda cewa zan iya rubutu da karatu da goga kafaɗa da sauran marubuta takwarorina a ko’ina na samu kaina. Na samu ƙarfafa gwiwa da tallafi daga kowacce fuska, daga shugabanni da membobi na wannan ƙungiya, saboda matsayina na ƙaramar marubuciya, babu abinda nake buƙata sai ja a jiki da ƙarfafa gwiwa, kuma Alhamdulillah na samu a cikinta. Sannan na yi rijista da babbar ƙungiyar marubuta ta kasa wato ANA, kuma alhamdulillah a nan ma na ga abubuwa da dama na karamci da girmamawa da ƙarfafa gwiwa, fiye da yadda na tsammata.
Yaya ki ka ji da nasarar da ki ka samu a Gasar zauren Marubuta, wanne labari ne ya baki nasara?
Gaskiya na ji mamaki marar misaltuwa duk da nasan shi komai nufi ne na Allah.
Ban taɓa tsammanin labarina mai taken ‘Allura Ta Tono Garma’ zai zo ko da na ashirin ba, duba da manyan marubutan da suka shiga gasar, amma Alhamdulillah na ji daɗi, wanda baki ba zai iya furtawa ba, sai dai kawai na ce, Alhamdulillah!
Wanne saƙo ne labarin yake koyarwa?
Dama gasar an bada jigon ta akan bincike ne, illarsa da amfaninsa. Don haka na ɗauki illar bincike, inda na yi bayani akan illar mutum ya riƙa ƙoƙarin binciko laifi ko kuskuren ɗan uwansa.
Mene ne ra’ayinki game da gasar rubutu na wata-wata da sauran shirye-shirye wanda zauren Marubuta ke shiryawa?
Gaskiya irin tsare-tsaren da wannan bijimin zaure na Marubuta, yake zuwa da su, ba ƙaramin ƙarfafa gwiwa suke yi ba, musamman ga marubuta masu tasowa, saboda da irin waɗannan ƙananan gasassakin ne ƙaramin marubuci yake samun gogewa har zuwa babbar gasa. Na jima da faɗin cewa ba komai ya sa wannan zaure ya yi fintinkau ga sauran takwarorinsa ba, sai ɗaukar wannan salon shirye-shiryen da ba kowanne zaure za ka je ka same su ba. Allah Ya ƙara nasarori da ƙwarin gwiwa ga jagororin wannan zaure da sauran zaurukan mu na marubuta a duk inda suke.
Wanne abu ne ya fi birgeki game da rayuwar marubuta?
Haɗin kai! Haƙiƙa abin yana matuƙar burgeni yadda marubuta ke da haɗin kai a duk inda aka haɗu ko da ba a san juna ba. Duk da wani lokacin akan samu masu kallon duk wanda basu sani ba a matsayin bare, amma dai masu sauƙin kan sun fi yawa.
Me ki ke fara tunani kafin ki rubuta labari?
Ina duba matsalar da tafi addabar mu ne, ko matsalolin da suke kusa da mu, ko wani sabon al’amari da na ga ya faru ko yake faruwa, sai na yi rubutu akai.
Wanne irin salon rubutu ne ya fi birgeki, almara, soyayya, tarihi ko zamantakewa?
Gaskiya ban damu da wani rubutu akan soyayya ba yanzu, kasancewar na fahimci har kullum mutane na buƙatar sababbin abubuwa ne, shi kuma rubutun soyayya abu ne da ya sha jagwalgwalo a hannun marubuta tun kafin a haife mu. Don haka ni na fi son rubutu akan laifuffuka, almara da zamantakewa.
A wanne lokaci ki ka fi samun natsuwar rubutu, safiya ko dare?
Gaskiya duk lokacin da nake ni kaɗai ina iya rubutu ko dare ko safiya ko yamma. Kawai idan ina jin yunwa ko damuwa ko zafi ko tsananin sanyi shi ne bana iya rubutu, amma wani lokacin ko da ana hayaniya kusa da ni matuƙar dai ba da ni ake maganar ba, zan iya rubutuna.
Idan shugaban Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i na Jihar Kano, ya nemi shawararki kan yadda za a inganta harkar rubutun adabi a Kano, me za ki gaya masa?
Bai wa ɓangaren adabi gudunmawa kamar yadda ake bai wa kowanne ɓangare. Zan so a ce Hukumar ta riƙa jan marubuta a jiki ana jin matsalolinsu da abubuwan da ke kawo naƙasu ga cigaban ayyukansu, saboda Hausawa sun ce mai ɗaki shi yasan inda ke masa yoyo. Sannan mu ma marubuta mu bada goyon baya ga dukkan dokoki da umarnin gwamnati don a riƙa kowacce tafiya da mu da ayyukanmu.
A cikin rubutunki wanne ne ki ka buga ko ki ke shirin bugawa?
Ban taɓa buga wani littafina ba, sai dai nan da wani lokaci kaɗan kamar yadda na faɗa a baya, zan fitar da littafina na farko da zan yi talifi, wato TAURARUWA, wanda nake fatan ya zamo silar haskawar tawa tauraruwar nima, in sha Allahu.
Wanne buri ki ke da shi nan gaba a harkar rubutu?
Buri na shi ne na samu ɗaukaka da shahara (Amma ba irin shaharar Zaitun jarumar labarin Tauraruwa ba). Ina da burin na zamo marubuciyar da zan samu damar da zan bada tallafi ga marubuta masu tasowa, saboda nasan wahalar dake cikin gwagwarmayar zama wani, da raɗaɗin dake cikin rashin tallafi daga wanda kake ganin yana da damar tallafa maka.
Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?
In da rai da rabo, watarana jinjiri ma ango ne!
Na gode.
Masha Allah. Ni ma ina godiya.
