Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin sarakunan Rano, Gaya da ƙaraye masu daraja ta biyu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a Kano, sabbin sarakunan za su kasance a matsayi na biyu da Sarkin Kano a matsayin daraja na ɗaya.
Sabbin sarakunan da aka nada sune:
Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin ƙaraye (wanda har zuwa lokacin naɗa shi Hakimin Rogo).
Alhaji Muhammad Isa Umar a matsayin Sarkin Rano (wanda har zuwa lokacin naɗa shi Hakimin Bunkure).
Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya (wanda shine sarkin rusasshiyar masarautar Gaya).
A lokacin da yake taya sabbin Sarakunan murna, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarce su da su kasance masu kula da al’adu da zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Masarautun nasu.
Zaku iya tuna cewa a jiya ne 16 ga watan Yuli, 2024 Gwamnan ya rattaɓa hannu a kan kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar.
