Shahararren mawaƙin Hausa, Dauda Adamu, wanda aka fi sani da Rarara, ya bayyana yadda wani Kirista da aka yi garkuwa da shi ya ɗauki nauyin kula da mahaifiyarsa, Hauwa Adamu, a lokacin da ake tsare da ita wajen masu garkuwa.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an sako mahaifiyar tashi mai shekaru 75 a ranar Alhamis bayan ta shafe kusan makonni uku a hannun wanda su ka yi garkuwa da ita.
A wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta a ranar Asabar, Rarara ya godewa ‘yan Nijeriya bisa addu’o’i da fatan alheri da suka yi a lokacin da mahaifiyarsa ta shiga mawuyacin hali.
Ya kuma yaba da ƙoƙarin shugaba Bola Tinubu, Uwargidan shugaban ƙasa Remi Tinubu, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin tsaro, Shehu Buba da wasu fitattun ‘yan Nijeriya bisa ƙoƙarinsu na ganin an sako mahaifiyarsa.
Abin da ya fi burge ni shi ne yadda wani Kirista ya zaɓi ya ci gaba da zama a bauta domin ya kula da mahaifiyata. An yi garkuwa da shi ne wata guda da ya gabata kuma an biya ƙuɗin fansar shi, amma ya ki ya tafi.
“Lokacin da yaga mama tana kuka, sai ya dage ya zauna har sai an sallami Mama, kuma ya ƙara sati biyu domin ya kula da ita.
“Abin mamaki shi ne, mutumin nan ba ma addini ɗaya da mama yake ba. Na gode muku da gaske, kuma ina roƙon Allah ya saka muku da alheri,” inji shi.
Ya kuma ce gwamnati na iya bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar rashin tsaro a ƙasar.
